in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Cibiyoyin fasahar zamani su ne tushen ci gaban kirkire kirkiren kasar Sin
2018-12-27 10:22:17 cri

Ministan kimiyya da fasaha na kasar Sin Wang Zhigang, ya sanar a jiya Laraba cewa, manyan cibiyoyin fasahar zamani na kasar Sin sun taka muhimmiyar rawa wajen bunkasa fannin kirkire kirkire na kasar cikin shekaru 30 da suka gabata.

Manyan cibiyoyin fasahar, wadanda yawansu ya kai 168, sun kasance wasu muhimman ginshikai wadanda suka taimaka wajen ci gaban tattalin arzikin kasar Sin, Wang ya bayyana hakan ne a birnin Beijing, a lokacin bikin cika shekaru 30 da kafuwar manyan cibiyoyin fasahar zamani na kasar Sin.

A shekarar 2017, a cibiyoyin fasahar zamanin kasar, an kafa masana'atun dake amfani da fasahohin zamani kimanin 52,000, wadanda suka kai kashi 38.2 bisa 100 na dukkan masana'tun kasar. Adadin kudaden shigar da cibiyoyin fasahar suka samar ya kai kudin Sin yuan trillion 30.7 kwatankwacin dalar Amurka trillion 4.46, kana karfin tattalin arzikin GDP da suka samar ya kai yuan trillon 9.52, wanda ya kai matsayin kashi 11.5 bisa 100 na jimillar GDP na kasar.

Yawan kayayyakin da masana'antun cibiyoyin suka fitar ketare ya kai dala biliyan 478 a shekarar 2017, kusan kashi 20 bisa 100 na adadin da kasar ta samu a fannin.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China