in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mutane 3 sun ji rauni sakamakon harin da Isra'ila ta kai a Syria
2018-12-26 13:26:38 cri

Bisa labarin da aka samu a jiya Talata, an ce, a wannan rana da dare, kasar Isra'ila ta kai harin makamai masu linzami a kasar Syria, harin da ya hallaka wani gidan ajiye makamai, yayin da sojoji 3 suka jikkata.

Rundunar sojojin kasar Syria ta bayyana cewa, jiragen saman soja na Isra'ila sun kai hare-haren makamai masu linzami ga kasar Syria daga kasar Lebanon a daren ranar 25 ga wata. Kana, tsarin kiyaye tsaron kasa daga sama na kasar Syria ya harbo galibin makamai masu linzami na Isra'ila a yankin dake yammacin birnin Damascus, fadar mulkin kasar ta Syria.

A wannan rana da dare, dan jaridar kamfanin dillancin labarai na Xinhua ya yi ta jin babbar karar fashewar boma-bomai a birnin Damascus, kuma makamai masu linzami sun ci gaba da tashi a yammacin birnin, lamarin da ya dade har tsawon awa daya.

Kuma bisa labarin da kungiyar sa ido kan harkokin hakkin dan Adam a kasar Syria, wadda hedkwatarta take birnin London ta fidda, an ce, a daren ranar 25 ga wata, Isra'ila ta harba makamai masu linzami a yammacin birnin Damasucs, da yankunan karkara dake kudu maso yammacin kasar Syria, kuma burinta shi ne lalata gidan ajiye makamai na kungiyar Hezbollah.

Isra'ila ta dauki kungiyar Hezbollah wata babban kalubale ga tsaron kasar, kuma tana zargin cewa, kasar Iran ta samarwa kungiyar Hezbollah makamai ta kasar Syria. Shi ya sa, sau da dama, Isra'ila take kai hare-hare ga kasar Syria da nufin mayar da martani ga wannan kungiya. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China