in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Fashewar boma-bomai ta haddasa rasuwar mutane 2 a kudancin Somaliya
2018-12-26 11:17:16 cri
Jiya Talata, rundunar 'yan sandan kasar Somaliya ta bayyana cewa, a wannan rana, wasu boma-bomai sun fashe a wani titin dake birnin Baidao dake kudancin kasar, lamarin da ya haddasa rasuwar mutane 2, yayin da 13 suka jikkata.

Wani dan sandan kasar ya bayyana cewa, wasu matasa suna bikin gargajiya a lokacin fashewar boma-boman. Kuma wani mazauni yankin Ahmed Nur ya ce, a lokacin, ya ji babbar kara ta fashewar boma-bomai, sa'an nan mutane sun gudu. Kana, wurin da boma-boman suka fashe shi ne wurin da matasan wurin su kan yi bukukuwa.

Ya zuwa yanzu, babu wanda ya sanar da daukar alhakin kaddamar da wannan hari, amma, wasu suna ganin cewa, kungiyar al-Shabab ta kan kaddamar da irin wannan harin.

Kungiyar al-Shabab tana da alaka da kungiyar al-Qaeda, cikin 'yan shekarun nan, ta sha kaddamar da hare-haren ta'addanci a kasar Somaliya da ma sauran kasashen dake kewayen kasar. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China