in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Masanan Tanzaniya sun bayyana cewa sabuwar manufar Amurka kan Afirka ba ta dace da yanayin da nahiyar ke ciki ba
2018-12-26 11:19:11 cri

A ranar 13 ga wata, gwamnatin kasar Amurka ta fitar da sabuwar manufarta kan kasashen Afirka, kuma mai taimakawa shugaban kasar kan harkokin tsaron kasar John Bolton, ya gabatar da wani jawabi a wannan rana, inda ya bayyana cewa, sabuwar manufar da Amurka zata dauka kan kasashen Afirka zata ci gaba da mayar da kasar ta Amurka a matsayin kasa mafi muhimmanci a fadin duniya, haka kuma zata rage tasirin da kasashen Sin da Rasha ke kawowa kasashen dake nahiyar ta Afirka, amma wasu masanan kasar Tanzaniya sun nuna shakku kan wannan sabuwar manufa wadda take da niyyar kara karfafa huldar dake tsakanin Amurka da kasashen Afirka, inda suka bayyana cewa, manufar bata dace da hakikanin yanayin da kasashen Afirka ke ciki a halin yanzu ba.

Mai taimakawa shugaban kasar Amurka kan harkokin tsaron kasa John Bolton ya bayyana cewa, sabuwar manufar da Amurka zata aiwatar yayin gudanar da huldar dake tsakaninta da kasashen Afirka tafi mai da hankali kan hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya dake tsakanin sassan biyu, haka kuma tafi maida hankali kan aikin dakile ayyukan ta'addacin da kungiyar IS da sauran kungiyoyin masu tsattsauren ra'ayi suke gudanarwa a kasashen Afirka, amma shahararren mai yin sharhi kan harkokin kasashen duniya da suka fi jawo hankalin jama'a na kasar Tanzaniya Francis Semwaza yana ganin cewa, abubuwan da Bolton ya bayyana a cikin jawabinsa basu da ma'ana, saboda daga cikin su, sabuwar manufar Amurka bata nuna hakikanin shirin gudanar da hadin gwiwa dake tsakanin sassan biyu, yana mai cewa,"Ba mu gane ba saboda sabuwar manufar Amurka bata bayyana sabon shirin gudanar da hadin gwiwar dake tsakanin Amurka da kasashen Afirka ba, ana iya cewa, babu bambanci dake tsakanin tsohuwar manufar da sabuwar manufar, kana abu mafi muhimmanci shine a cikin sabuwar manufar da gwamnatin Amurka ta fitar, ba a bayyana hakikanan matakan da Amurka zata dauka a fannin kara karfafa hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya dake tsakaninta da kasashen Afiirka ba, misali duk da cewa, Amurka ta nuna fatanta cewa, tana son kara karfafa hadin gwiwa da kasashen Afirka, amma bata bayyana ta wace hanya ce zata cimma wannan burin ba, a don haka ina ganin cewa, sabuwar manufar bata da ma'ana."

A cikin jawabinsa, Bolton ya bayyana cewa, yanzu kasashen Sin da Rasha suna yin gogayya ne da Amurka a nahiyar Afirka, kuma ya ce, Sin da Rasha sun lalata moriyar Amurka a Afirka, har ya zargi huldar dake tsakanin Sin da Afirka kamar yadda yake so, kan wannan Semwaza ya bayyana cewa, daga jawabin da Bolton ya gabatar, an lura cewa, har kullum Amurka tana mayar da kanta a matsayin kasa mafi muhimmanci a fadin duniya, haka kuma an lura cewa, Amurka ta fitar da manufa irin ta tunanin yakin cacar baka, wato yakin sanyi, a cewarsa, "Daga manufar da Amurka ta fitar, mun lura cewa, watakila Amurka tana son kasashen Afirka su zaba, wato idan suna son raya hulda da Amurka, to dole ne su daina yin cudanya da kasashen Sin da Rasha, Amurka tana ganin cewa, idan ta zuba jari a Afirka, hakika tana mayar da moriyarta a gaban kome, amma muna ganin cewa, idan ana gudanar da hadin gwiwa tsakanin sassan biyu, dole ne su samu moriya tare. Muna fatan Amurka ta lura cewa, Afirka ta riga ta samu ci gaba, ya kamata ta gudanar da hadin gwiwa dake tsakaninta da sauran kasashen duniya daga dukkan fannoni."

A nasa bangare, shahararren marubucin Tanzaniya Makwaia Kuhenga shi ma ya bayyana cewa, ya kasance zumunta mai dogon tarihi dake tsakanin kasashen Sin da Tanzaniya, ba zai yiwu ba a gurgunta zumuntar, kana al'ummomin kasashen Afirka suna da ikon zaben abokansu, kana ya yi kira ga kasashen Afirka dasu ci gaban da raya kasashensu ta hanyar dogaro kan karfinsu, yana mai cewa, "Kasar Sin ta samar da taimako ga kasashen Afirka ne domin tabbatar da samun moriya tare, kasashen Afirka su ma suna maraba da taimakon da kasar Sin take samarwa, saboda mun gano cewa, ba zai yiyu ba kasar Sin ta tilasta mana mu yi aikin da bamu so mu yi ba, amma kila ne wasu kasashen yamma suna yin hakan, kana ina ganin cewa, ya zama dole kasashen Afirka su nace ga manufar raya kasa ta hanyar dogaro kan karfin kansu, kasar Tanzaniya ita ma haka take, har kullum tana aiwatar da manufar diplomasiyya irin ta 'yan ba ruwanmu da dogaro kan karfin kanta, to dalilin da ya sa kasarmu ta zabi kasar Sin domin su gudanar da hadin gwiwa, shine domin tana ganin cewa, gwamnatin kasar Sin tana daukan hakikanan matakai yayin da take aiwatar da hadin gwiwa dake tsakaninta da sauran kasashe masu tasowa, ba tare da gindaya kowane irin sharadi na siyasa ba, a don haka idan an ce, dole mu daina hulda da kasar Sin, ba zai yiwu a cimma wannan makarkashiyar ba har abada."(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China