Jami'an gwamnatin 56 suna aiki ne a yankin jahar Oromia na kasar, yankin wanda ke shiyyar tsakiyar kasar, ana zarginsu ne da rashin tafiyar da ayyukansu bisa ka'ida da kuma yin almubazzaranci da dukiyar gwamnati, kafar yada labarai ta yankin Oromia (OBN) ne ta bada rahoton.
Hukumar yaki da rashawa ta yankin Oromia tana shirin sake damke wasu jami'an nan da wasu kwanaki masu zuwa, in ji OBN.
A watan Nuwamba, kasar Habasha ta kama wasu manyan jami'an sojojin kasar, wadanda take zarginsu da hannu a ayyukan cin hanci da rashawa.
Kama mutanen, yana daga cikin muhimman matakan yaki da rashawa da cin zarafin bil adama, kuma yana daga cikin muhimman alkawurran da gwamnatin sabon firaiministan kasar Ahmed Abey ta yi ga al'ummar kasar, tun bayan nada shi a mukamin firaiministan a watan Afrilun wannan shekara. (Ahmad Fagam)