in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Buhari Zai Fara Kamfen Dinsa Daga Akwa Ibom
2018-12-26 10:40:19 cri
Bisa labarin da jaridar Leadership A yau ta bayar a shafinta na intanet, an ce, Shugaban tarayyar Najeriya Muhammadu Buhari zai fara kamfen dinsa na neman tazarce a zabe mai zuwa a ranar Jumma'a, 28 ga watan Disamba.

Zai fara kamfen dinsa daga garin Uyo, babban birnin jihar Akwa Ibom. Babban mai ba shugaban kasa shawara a kan harkokin majalisa, Sanata Ita Enang ne ya bayyana hakan a ranar Litinin 24 ga watan Disamba yayin da yake jawabi ga manema labarai a Uyo.

Enang ya bayyana cewa shugaban kasa zai kasance a jihar tare da shugaban jam'iyyar na kasa Kwamrad Adams Oshiomhole da kuma babban jigon jam'iyyar. Ya kuma bayyana cewa jam'iyyar za ta yi amfani da damar wajen gabatar da tutar jam'iyyar ga 'yan takarar gwamna na APC a jihohin Akwa Ibom, Cross River da Delta. (Leadership A Yau)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China