Da yake tabbatar da hakan, kakakin hukumar tunkarar bala'u ta kasar Sutopo Nugroho, ya ce aman wuta da tsaunin Anak Krakatau ya yi a daren ranar Asabar, shi ne ya haifar da ambaliyar. Ya ce bala'in ya lalata gidaje 882, da Otal 73, da sauran wasu gine gine da dama. Kaza lika ambaliyar ta raba mutane 16,082 da gidajen su.
Ma'aikatan ceto na ci gaba da laluben wadanda wannan ibtila'i ya shafa a ruwa da sassan tudu, musamman a zirin da ke tsakanin tsibiran Java da na Sumatra, kasancewar akwai zaton igiyar ruwa mai karfi ta yi awon gaba da mutane da dama.