Rahotannin sun ce, yayin da shugaban kasar Rwanda Paul Kagame ke zantawa da kafofin watsa labarai kwanakin baya a Vienna, babban birnin kasar Austria, ya ce, mu'amalar dake tsakanin Sin da Afirka abu ne mai kyau. Ya ce Sin na nuna himma da kwazo wajen gudanar da ayyukan hadin-gwiwa a Rwanda amma ta hanyar da ta dace. Kagame ya ce, kasashen Afirka sun san karfin da suke da shi, da kuma wadanne irin shawarwari ne ya kamata su amince da su daga kasar Sin, don haka ba za su tsunduma cikin basusuka masu tarin yawa ba.
Shugaba Kagame ya kara da cewa, wannan ya danganta da mutanen Afirka, su ne kuma suka san yaya za su yi hadin-gwiwa tare da kasar Sin. Haka kuma, irin rashin gaskiya da wasu Turawa suke nunawa ya ba shi mamaki sosai.(Murtala Zhang)