in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sabuwar siffar kasar Sin
2018-12-25 21:34:17 cri

A kwanan nan, a yayin babban taron MDD, an zartas da wani sabon kuduri cewa, yawan kudin mamba da kasar Sin za ta samarwa MDD tsakanin shekarar 2019 da ta 2021 zai karu zuwa kashi 12.01% daga 7.92% na yanzu, sannan yawan kudin tabbatar da zaman lafiya a duk duniya da kasar Sin za ta kebewa MDD zai karu zuwa kashi 15.2%. Kudurin ya sa kasar Sin ta zama kasa mafi girma ta biyu wajen biyan kudin mamba na MDD da aikin tabbatar da zaman lafiya da MDD take yi a duk fadin duniya. Game da wannan sabuwar siffar da kasar Sin take da ita a gamayyar kasa da kasa, mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ya bayyana cewa, wannan ne sakamakon karuwar jimillar GDP ta kasar Sin da matsakaicin kudin shiga na al'ummar Sinawa, ya kuma alamta karuwar tasirin kasar Sin a duk duniya.

Bana shekara ce ta cika shekaru 40 da kasar Sin ta kaddamar da manufar yin gyare-gyare a gida da bude kofarta ga ketare, matsakaicin karuwar tattalin arzikinta a duk shekara ya kai kashi 9.5% ya sa kasar Sin ta kubutar da kanta daga kangin talauci zuwa sabon yanayin dake da matsakaicin karfin tattalin arziki a duniya.

A cikin shekaru goma da suka gabata, gaba daya kasar Sin ta tura tawagogin jiragen ruwan soja har sau 31 domin gudanar da aikin tabbatar da tsaro ga jiragen ruwan jigilar kayayyaki na kasar Sin da na sauran kasashen duniya guda 6595 da suke tafiya a gabar tekun Aden da kuma gabar tekun Somaliya, inda suka ceci jiragen ruwan da suka gamu da hadurra sama da 60, kana sun kammala ayyuka daban daban kan teku cikin nasara, misali kwashe Sinawan dake zaune a kasashen Libya da Yemen da suka gamu da hadari zuwa nan gida kasar Sin, da samar da tsaro ga jiragen ruwa masu jigilar makaman kare dangi na kasar Syria domin rushe su a kasar waje, da aikin neman jirgin saman kasar Malaysia wanda ya bace a shekarar 2014, da aikin samar da ruwa ga mazauna birnin Male na kasar Maldives cikin gaggawa da sauransu. Ban da haka, bisa matsayinta na daya daga cikin kasar dake da wakilcin din din din a kwamitin MDD mai kasashe biyar na wadda sojojin kiyaye zaman lafiyar da ta turawa kasashen waje sun fi yawa, kasar Sin ta taba shiga ayyukan kiyaye zaman lafiya har sau 30, a sanadin haka zamantakewar al'ummar kasashen duniya sun mayar da kasar Sin a matsayin kasa mafi mihimmanci wajen kiyaye zaman lafiya wadda ta tabbatar da zaman lafiya a fadin duniya.

A shekarar 2013, shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya gabatar da shawarar "Ziri Daya da Hanya Daya", inda ya gabatar da wasu sabbin ra'ayoyi, domin kyautata aikin kula da duniyarmu. Koda yake, wasu kasashen dake yammacin duniya suna tsoron ganin kasar Sin ta kara zama mai fada a ji a duniya, don haka suna ta kokarin shafawa shawarar kashin kaji. Duk da haka, cikin shekaru 5 da suka wuce, wasu kasashe da yankuna fiye da 100 sun nuna goyon baya ga shawarar, gami da kokarin shiga cikin ayyuka masu alaka da shawarar, sa'an nan wasu kasashe da kungiyoyin kasa da kasa fiye da 70 sun kulla yarjejeniyar hadin gwiwa da kasar Sin don shiga shawarar ta "Ziri Daya da Hanya Daya".

A kasar Habasha, wata kasar da wasu kafofin watsa labaru na kasashe daban daban suka ba ta lakabi na "Kasar Sin dake nahiyar Afirka", an samu karuwar kamfanonin kasar Sin dake zuba jari a kasar. Alkaluman da aka samu daga kwamiti mai kula da aikin zuba jari na kasar sun nuna cewa, tsakanin shekarun 2012 da 2017, baki daya an samu kamfanonin kasar Sin 279 da suke gudanar da ayyuka a kasar Habasha, inda suka samar da guraben aikin yi 28300, da taimakawa kasar don ta kiyaye karuwar tattalin arzikinta fiye da kashi 10% a shekarun nan.

Jaridar Daily Nation ta kasar Kenya ta bayar da sharhi a watan Satumbar bana, cewar kasar Sin wata abokiyar hadin kai ce mai daraja ga kasashen Afirka, wadda ta yi kokarin kawar da talauci da ta dade take fuskanta cikin wasu 'yan karnoni. Maganar "tarkon bashi" da kasashen yamma suka yi ba domin fatan ciyar da kasashen Afirka gaba ba ne. A matsayinta na kasar da ta fi cin basussuka a duniya, damuwar da kasar Amurka ke nunawa ba ta da tushe. A cikin sharhin, ana ganin cewa, nahiyar Afirka dake samun ci gaba za ta iya biyan basussukan da ta ci, don taimakawa jama'ar nahiyar wajen kawar da talauci, kamar yadda kasar Sin ta yi a cikin shekaru 40 da suka gabata.

Shahararriyar kungiyar kwararrun masana ta kasar Amurka Brookings Institution, ta bayar da rahoto cewa, ayyukan zuba jari da ci gaba za su iya kawar da matsalolin da ake fuskanta wajen neman ci gaba dake iya hade da kowa da kowa.

Rahoton ya ruwaito bincike da nazarin da wasu kwararru suka yi kan ayyukan zuba jari su 4300 da kasar Sin ta yi a kasashe 138, inda suka gano cewa, mafi yawancin ayyukan zuba jari da kasar Sin ta gudanar sun samar da moriya ga kasashe daban-daban. Kwararrun na ganin cewa, shekaru biyu ke nan bayan da aka amince da bada kudin, idan kasar Sin ta ninka yawan kudin da ta zuba a wadannan kasashe, tattalin arzikinsu zai karu da kashi 0.4 bisa dari. Shi ya sa ana iya cewa, Sin babbar kasa ce dake bayar da gudummawa ga bunkasuwar duk duniya baki daya.

A shekara ta 2018, ra'ayin nuna fin karfi kan sauran kasashe da ra'ayin bada kariya ga harkokin kasuwanci na dada bazuwa a duniya, al'amarin da ya haifar da babban kalubale ga doka da oda da tsarin kasuwancin duniya da aka kafa tun bayan da aka gama yakin duniya na biyu. Takaddamar cinikayyar da kasar Amurka ta janyo na kara haifar da tashin hankali ga kasuwar hannayen jari ta duniya, da rage imanin da ake da shi, tare kuma da kawo cikas ga ci gaban tattalin arzikin duniya.

A halin da ake ciki na fuskantar rashin tabbas ta fannin tattalin arziki, ana cikin wani muhimmin lokaci na yin gyare-gyare ga tsarin kula da harkokin duniya, kuma kasa da kasa na kara damuwa da makomarsu. Kasashen duniya na bukatar wani jagoran da zai iya ba su jagoranci ta fannin samun ci gabansu, jagoran da ba wai don ya fi karfin wani ba. Kasar Sin ba ta son maye gurbin kasar Amurka ta wasu fannonin da take jagoranta, kuma ba ta son kalubalantarta. Wannan jagoranci ya dogaro ne kan 'yan siyasa na kasa da kasa za su iya raya sabon tsarin huldar kasashen duniya na mutunta juna da nuna adalci da kuma hadin gwiwar samun moriyar juna, a maimakon irin na nuna fin karfi ga wani bangare.

Kasar Sin za ta zama kasa ta biyu wadda ta fi biyan kudin mambar MDD da kuma kudin kiyaye zaman lafiya, shi ya sa, mutanen kasa da kasa suka yi hasashen cewa, bisa sakamakon da kasar Sin ta samu, da kuma gudummawar da ta baiwa kasa da kasa cikin shekaru 40 da suka gabata, kasar Sin za ta ci gaba da yin hadin gwiwa da kasa da kasa domin gina makomarmu mai zaman lafiya, mai tsaro, mai wadata da kuma mai nuna fahimtar juna. Haka kuma, kasar Sin ba za ta bata moriyar kasashen ketare domin neman bunkasar kanta ba, kana ba za ta dakatar da kare ikonta yadda ya kamata ba. A nan gaba kuma, kasar Sin za ta ci gaba da dukufa wajen kiyaye zaman lafiyar kasa da kasa, da neman ci gaban kasashen duniya da kuma kare tsarin kasa da kasa. (Sanusi Chen, Jamila Zhou, Bello Wang, Bilkisu Xin, Murtala Zhang, Lubabatu Lei, Maryam Yang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China