Madam Hua ta bayyana haka ne a yayin taron manema labaru da aka shirya a jiya Litinin, inda ta ce, jama'ar kasar Canada Michael Kovrig da Michael Spavor sun aikata laifukan kawo illa ga tsaron kasar Sin, ko shakka babu hukumomin da abun ya shafa na kasar Sin su dauki matakai masu tsanani kan su bisa doka.
Game da damuwar da kasar Burtaniya da kungiyar EU suka nuna kan mutanen biyu da ake tsere da su a makon da ya wuce, madam Hua ta ce, a hakika dai sun dauki ma'auni biyu kan hakkin bil Adama. Da ma kasar Canada ta tsare babbar jami'ar wani kamfanin kasar Sin bisa bukatar kasar Amurka, wadda har ma kasar Canada ta amince da cewa ba ta sabawa kowace irin doka ba, wannan mataki shi ne ainihin aikin tsarewa ba bisa doka ba. (Bilkisu)