in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kotun sojan Somalia ta yanke hukuncin kisa ga wani dan kungiyar al-Shabab
2018-12-25 10:28:42 cri
Kotun sojan kasar Somalia ta yanke hukuncin kisa kan wani dan kungiyar al-Shabab bisa zarginsa da hannu cikin wasu hare-haren bom, wadanda suka yi sanadiyyar rasa rayukan mutane fiye da 10.

Abdullahi Bule, mai gabatar da kara a kotun, ya gayawa manema labaru hakan a jiya Litinin. Ya ce, kotun ta tabbatar da laifin dan kungiyar al-Shabab din mai suna Abdulkadir Abubakar, bisa yadda ya taka muhimmiyar rawa a wasu jerin hare-haren bom da aka kai birnin Mogadishu, cikinsu har da wani da aka kai hotel din Wehliye a watan Maris na bara, wanda ya kashe mutane 10, da jikkatar wasu 17.

Jami'in ya ce, an kama mutumin ne yayin da yake tuka wata mota mai dauke da boma-bomai a yankin Hamarwayne, a watan Mayun shekarar 2017. Tun daga lokacin, kotun ta riga ta yi zama har karo 3 don tantance laifin da mutumin ya aikata. (Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China