Game da haka, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin madam Hua Chunying, ta ce kasar Sin za ta samar da tallafi ga kasar Indonesia a fannin aikin ceton da ake yi game da wannan bala'in, ta hanyar kungiyar agaji ta red cross da dai sauransu.
Hua Chunying ta bayyana hakan ne, yayin taron manema labaru da aka shirya a yau Litinin. (Bilkisu)