in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sakatare janar na MDD ya nuna damuwarsa game da hasarar rayuka sakamakon bala'in ambaliyar ruwan teku na Tsunami a Indonesiya
2018-12-24 11:27:33 cri
Sakatare-janar na Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres ya nuna matukar rashin jin dadi game da mutanen da suka rasa rayukansu ko jin raunuka da hasarorin da aka tafka sakamakon iftila'in ambaliyar ruwan teku da ake kira Tsunami wanda ya shafi tsibirin Sumatra na kasar Indonesiya a ranar Asabar din da ta gabata, a cewar ofishin yada labarai na sakatare-janar din.

Antonio Guterres ya jajantawa iyalan wadanda suka mutu da kuma gwamnati gami da jama'ar kasar Indonesiya, inda ya yi fatan samun sauki cikin sauri ga wadanda suka samu raunuka a yayin ibtila'in.

Har wa yau, MDD a shirye take wajen samar da tallafi da goyon-baya ga ayyukan ceto da gwamnatin Indonesiya ke kokarin gudanarwa. (Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China