in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta shawarci a ingiza ci gaban makamashi a Afirka
2018-12-24 10:59:01 cri

A ranar 22 ga wata, an shirya taron shugabannin kasashe mambobin kungiyar ECOWAS karo na 54 a Abuja, fadar mulkin tarayyar Najeriya, inda gwamnatin kasar Guinea da kungiyar hadin kai tsakanin kasa da kasa ta ci gaban makamashi wato GEIDCO da hukumar kungiyar ECOWAS suka shirya wani taron manyan jami'ai cikin hadin gwiwa domin tattauna shawarar da kasar Sin ta gabatar game da kafa wata kungiyar ingiza ci gaban makamashi a kasashen Afirka, domin sa kaimi kan dauwamammen ci gaban tattalin arziki da zamantakewar al'umma da makamashin wutar lantarki a nahiyar baki daya.

A ranar 26 ga watan Satumban shekarar 2015, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da wata shawara game da kafa wata kungiyar hada kai tsakanin kasa da kasa ta fuskar samar da makamashi a yayin taron kolin MDD da aka shirya domin tattaunawa kan batun ci gaban kasashen duniya, shawarar ta samu karbuwa matuka daga al'ummomin kasashen duniya baki daya. Hakika makasudin kafa kungiyar shine domin samar da makamashin wutar lantarki mai inganci ta hanyar yin amfani da fasahar zamani da makamashi mai tsabta ga daukacin al'ummomin kasashen duniya. Ya zuwa watan Nuwamban shekarar 2017, an shigar da shirin nan cikin muradun tabbatar da dauwamammen ci gaba na MDD nan da shekarar 2030.

An kafa kungiyar hada kai tsakanin kasa da kasa ta fuskar samar da makamashi wato GEIDCO ne a watan Maris na shekarar 2016, domin kara karfafa hadin kai dake tsakanin kasa da kasa a fannin samar da makamashin wutar lantarki, ta yadda za a biya bukatun amfanin wutar lantarki mai tsabta a fadin duniya. Yayin taron manyan jami'an da aka gudanar a Abuja, shugaban kungiyar hada kai tsakanin kasa da kasa ta fuskar samar da makamashi Liu Zhenya ya gabatar da wani jawabi, inda ya yi bayani kan shirin raya makamashi a yankin yammacin Afirka ga shugabannin kasashen yammacin Afirka da sauran manyan jami'an wadanda suka halarci taron, yana mai cewa, "Mun yi nazari sosai kan albarkatun hallitu da ci gaban masana'antu da bukatun wutar lantarki na kasashen dake yammacin Afirka, daga baya mun tsara shirin hadin gwiwa don samar da makamashi a kasashen, a takaice ana iya cewa, za a yi amfani da albarkatun halllitu, tare kuma da kara karfafa hadin gwiwa dake tsakanin kasa da kasa domin samar da makamashi mai tsabta ga kasashen dake yammacin Afirka, tare kuma da biyan bukatun ci gaban tattalin arziki da zamantakewar al'umma a kasashen yadda ya kamata."

Ana gudanar da aikin hada kai tsakanin kasa da kasa ta fuskar samar da makamashi bisa matakai uku ne, wato hada kai a cikin gida, da hada kai tsakanin kasashen dake cikin nahiya, da kuma hada kai tsakanin kasa da kasa a fadin duniya, ana sa ran cewa, za a kammala aikin nan da shekarar 2050. Bisa shirin da aka tsara, hada kai dake tsakanin kasashen Afirka wajen samar da makamashi shi ma yana da muhimmanci matuka yayin da ake kokarin tabbatar da shirin hada kai tsakanin kasa da kasa, Liu Zhenya ya bayyana cewa, "Ana iya tabbatar da hada kai tsakanin kasashen Afirka ne ta hanyar yin amfani da fasahar zamani, daga baya ana iya cimma burin tabbatar da ci gaban wutar lantarki da masana'antu da cinikayya da hakar ma'adanai, hakan zai sa kaimi ga cigaban kasashen Afirka kamar yadda ake fata."

Yayin taron, an yi kira ga kasashen dake yammacin Afirka dasu shiga kawancen tabbatar da dauwamammen ci gaba ta hanyar hada kai wajen samar da makamashi tsakanin kasashen Afirka, wanda gwamnatin kasar Guinea da kungiyar hada kai tsakanin kasa da kasa ta fuskar samar da makamashi suka bada shawarar a kafa shi cikin hadin gwiwa, makasudin kafuwarsa shine domin samar da wani dandali ga kasashen Afirka domin su gudanar da hadin gwiwa tsakanin gwamnatoci da kamfanoni da hukumomin harkar kudi, tare kuma da ciyar da kasashen gaba yadda ya kamata.

Mai sulhuntawa na kawance kuma shugaban kasar Guinea Alpha Conde ya ce, "Afirka zata kasance wata babbar kasuwa, hada kai ba ma kawai zai ciyar da cinikayyar dake tsakanin kasashen Afirka gaba bane, har ma zai kyautata salon ci gaban aikin gona na kasashen, haka kuma zai ciyar da aikin bada ilmi da fasaha da masana'antu gaba."

Kwamishinan makamashi da aikin haka ma'adinai na kungiyar ECOWAS Sediko Douka yana ganin cewa, shawarar gudanar da hada kai wajen samar da makamashi tsakanin kasashen Afirka tana da ma'anar gaske, ya ce, "Aikin yana da muhimmanci matuka a gare mu, saboda muna fama da matsalar karancin makamashi, kuma bamu fara gudanar da hadin gwiwar dake tsakaninmu ba tukuna, a don haka muna bukatar a bamu shawara mai amfani a fannin."(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China