An yi tsammanin taron shugabannin kasashen kungiyar ta ECOWAS karo na 54 zai cimma matsaya wajen amincewar shigar kasar Morocco kungiyar.
Kasar Morocco ta gabatar da bukatar neman zaman mamba ta ECOWAS ne bayan da ta koma kungiyar tarayyar Afrika a watan Janairun shekarar 2017. An amince da kasar ta zama mambar AU ne a lokacin taron kolin ECOWAS a watan Yunin shekarar 2017, wanda ya gudana a Monrovia, babban birnin kasar Liberia.
An gabatar da bincike game da tasirin kasar na zama mamba a kungiyar daga bisani aka gabatarwa shugabannin kungiyar kasashen yammacin Afrika a taron kolin kungiyar karo na 52, wanda aka gudanar a watan Disambar 2017 a Abuja, inda shugabannin suka gaza cimma matsaya kan batun.
A halin yanzu, ECOWAS tana da mambobin kasashen yammacin Afrika 15, daga cikinsu babu wata kasa da ta hada kan iyaka da kasar Morocco, kasar wacce ke shiyyar arewacin Afrika. (Ahmad Fagam)