in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sharhi: Mene ne nufin Amurka na shigar da dokar "the Reciprocal Access to Tibet Act of 2018" cikin dokokin kasar
2018-12-22 18:37:11 cri
A 'yan kwanakin da suka wuce, fadar White House ta Amurka ta amince da dokar "the Reciprocal Access to Tibet Act of 2018" da aka zartas a majalisun dokokin kasar, dokar da ke da nufin kau da dukkan kayyadewa ga 'yan Amurka da suke son shiga jihar Tibet ta kasar Sin. Hakan ya sa aka shigar da dokar cikin dokokin kasar ta Amurka. Amincewa da dokar tamkar tsoma baki ne cikin harkokin cikin gidan kasar Sin da Amurkar ta yi, hakan kuma ya kasance yin zamba ne Amurkar ta yi wajen hana yaduwar ci gaban kasar Sin ba tare da la'akari da hakikanan abubuwa ba.

Bisa bukatun dokar ta "the Reciprocal Access to Tibet Act of 2018", dole ne gwamnatin kasar Sin ta amince da 'yan jarida, jami'an diplomasiyya da masu yawon shakatawa na kasar Amurka su shiga yankin Tibet na kasar Sin har illa masha Allahu, in ba haka ba, kasar Amurka za ta hana wadancan jami'an kasar Sin da suka tsara manufofi da hana Amurkawa shiga yankin Tibet su shiga Amurka. Dokar ta yi kamar tana nufin neman 'yancin Amurkawa don yin shigi da fice daga yankin Tibet na kasar Sin, amma a hakika dai, ta nuna wani ra'ayi ne irin na mallake duniya, wato "Amurka na da fifiko", kuma dokokin kasar Amurka na gaban dokokin kasa da kasa.

A ganin wadancan 'yan majalisun dokokin kasar Amurka da suka tsaya da gabatar da kuma jefa kuri'u don zartas da wannan dokar, babu wani wuri a duniya dake da ikon hana Amurkawa shigi da fice, Amurkawa za su iya zuwa ko ina da suke so. Amma, ba za a iya biyan dukkan bukatunsu ba, domin babu wata kasa dake yin maraba da wannan rashin girmamawa ga kasa da ka'idoji da kuma tsari.

Jihar Tibet, wata jiha ce da ba za a taba rabata daga kasar Sin ba, wannan tattaunawar da majalisar dokokin kasar Amurka ta yi ta sabawa ka'idar dangantakar diflomasiyya a tsakanin kasa da kasa, watau Amurka ta sake yin kutse a harkokin cikin gidan kasar Sin.

Alal hakika, kasar Sin ba ta taba hana mutanen ketare shiga jihar Tibet ba, bisa kididdigar da aka yi, an ce, a shekarar 2016, 2017 da kuma farkon watanni 11 na shekarar bana, yawan mutanen ketare da suka kai ziyara a jihar Tibet ya kai 321,900; 343,500 da kuma 381,400, ciki har da mutanen kasar Amurka sama da dubu 95. Haka kuma, wasu tawagogin wakilan majalisar dokokin kasar Amurka sun sha kai ziyara a jihar Tibet sau da dama.

Lamarin da ya nuna cewa, cikin shekarun baya bayan nan, yawan mutanen da suka kai ziyara a jihar Tibet yana karuwa. Kuma mutanen wajen da dama sun canja ra'ayoyinsu kan jihar Tibet, har wasu sun fara aiki da kuma zaman rayuwa a jihar sabo da kaunarsu kan wannan wuri. Wasu kuma, sun yi nazari kan al'adun jihar, har sun rubuta littattafai game da jihar da dama.

Hakika kasar Sin ba ta taba kayyade ziyarar da 'yan kasashen waje suke yi a yankin Tibet ba, maimakon haka, tana ta kokarin yada al'adu da tarihi na yankin, musamman ma ci gaban da yankin ya samu. Don janyo hankalin jama'ar kasashe daban daban, jihar Tibet mai cin gashin kanta ita ma ta gudanar da wasu ayyukan tallace-tallace, irinsu "ziyara a yankin Tibet a lokacin sanyi". Wadannan misalai ne dake shaida cewa, kofar kasar Sin, da kofar yankin Tibet, a bude suke, ana kuma maraba da zuwan baki na kasashen waje.

Ban da haka, domin taimakawa yankin Tibet a kokarinta na bude kofa, gwamnatin tsakiya ta kasar Sin ta mai da cikakken hankali kan aikin kyautata kayayyakin more rayuwa a yankin. Zuwa karshen shekarar bara, hanyoyin mota sun shiga cikin kashi 99% na kauyukan yankin Tibet, wadanda tsawonsu a baki daya ya kai kilomita dubu 90. Sa'an nan layukan zirga-zirgar jiragen sama da suka shafi jihar Tibet sun karu daga 37 zuwa 79. A fannin layin dogo kuma, tun bayan da aka kaddamar da layin dogo na Qinghai da Tibet a shekarar 2006, an fara gina sabon layi na Sichuan da Tibet. Yanzu a dukkan kauyukan yankin Tibet ana iya kama signar wayar salula, kana a kashi 85% na kauyukan ana iya hadewa da hanyoyin sadarwa na Internet masu sauri. Wadannan ci gaban da aka samu sun baiwa masu yawon shakatawa Sinawa da 'yan kasashen waje sauki matuka. Ban da haka kuma, kasancewar yankin Tibet kofar ciniki ce ta kasar Sin ga yankin Asiya ta Kudu, cinikayya na kara samun karuwa a yankin, musamman ma cikin shekarun baya.

A wajen taron taya murnar cika shekaru 40 da fara aiwatar da manufar gyare-gyare a gida da bude kofa ga kasashen waje a kasar Sin, wanda ya gudana a birnin Beijing, fadar mulkin kasar, a kwanan baya, shugaban kasar Sin Xi jinping ya furta cewa, wannan manufa ta kasance wata halayyar musamman ce ta kasar Sin, don haka al'ummar kasar za su tsaya kan wannan manufa har zuwa nan gaba. Don haka, ko shakka babu, yankin Tibet shi ma zai kara bude kofarsa, sai dai zai yi maraba ne da wadanda suka girmama Tibet, da kishin Tibet, da neman samun ci gaban Tibet, maimakon wasu mutanen da suke son tada rikici a yankin. Sa'an nan jama'ar yankin Tibet, su ma ba za su so su karbi wadanda ke neman yin amfani da wasu dokokin kasashen waje ba, irinsu "the Reciprocal Access to Tibet Act of 2018", wajen tsoma baki cikin harkokin gidan kasar Sin, da yunkurin tada zaune-tsaye a yankin Tibet. (Masu Fassarawa: Bikisu Xin, Maryam Yang, Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China