"Muna fata dukkannin bangarorin da abin ya shafa a Guinea-Bissau za su yi aiki tare domin tabbatar da ganin an gudanar da zaben cikin lumana kamar yadda aka tsara gudanarwa," inji Wu Haitao, mataimakain zaunannen wakilin kasar Sin a MDD. Ya bayyana hakan ne a taron kwamitin sulhun MDDr.
Zaben 'yan majalisar dokokin kasar ta Guinea-Bissau da farko an shirya gudanar da shi ne a ranar 18 ga watan Nuwamba, amma an dage shi sakamakon matsalar kalubalolin rashin kwararru. Sai dai shugaban kasar ta yammacin Afrika Jose Mario Vaz, a ranar Alhamsi ya fitar da wata doka, inda ya ayyana ranar 10 ga watan Mayun shekarar 2019 a matsayin sabuwar ranar gudanar da zaben kasar.
Wajibi ne alummomin kasashen duniya su kiyaye ikon mallaka da 'yancin cin gashin kai da martabar kasar ta Guinea-Bissau, inji Wu, ya kara da cewa, kasar Sin za ta yi aiki da sauran kasashen duniya wajen ci gaba da tattaunawa tsakanin dukkannin bangarorin da basa ga maciji da juna a Guinea-Bissau, domin tabbatar da samun dawwamamman zaman lafiya da kuma cigaban kasar ta yammacin Afrika baki daya. (Ahmad Fagam)