Kafar yada labaran kasar Canada a kwanan nan ta ba da rahotanni dake cewa hukumomin Amurka suna tuhumar wasu 'yan kasar Sin biyu inda ake zarginsu da satar bayanai ta kafar intanet.
Rahotannin sun kuma zargi kasar Sin da laifin yin kutse a kafar intanet ta kasar Canada, kana sun zargi kasar ta Sin da cewa ta saba alkawarin da ta dauka na kin yin amfani da kafar intanet wajen satar wasu bayanan sirri da suka shafi harkokin kasuwanci da fasahohi mallakin kamfanoni masu zaman kansu na kasar Canada.
"Kasar Sin ba ta taba daukar nauyin yin kutse a kafofin intanet na kasar Canada ba, ballanta ma ta ce wai za ta dakatar da duk wasu batutuwa dake da alaka da hakan. Wani ba zai yi alkawarin dakatar da abin da bai aikata ba," in ji sanarwar. (Ahmad Fagam)