in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin za ta ci gaba shirinta na neman ci gaba har sai ta samu nasara
2018-12-21 21:28:07 cri

A lokacin da kasar Sin take murnar cika shekaru 40 da aiwatar da manufar yin gyare-gayre a gida da bude kofarta ga waje, gamayyar kasa da kasa ta sake nuna sha'awarta ta neman dalilin da ya sa kasar Sin ta samu bunkasa cikin wadannan shekaru 40 da suka gabata, kuma mene ne ya sa kasar Sin ta kafa wannan abin al'ajabi a doron duniyarmu. Galibin masu fashin baki da kafofin watsa labaru na ganin cewa, kasar Sin ta samu ci gaba ne sakamakon kirkiro sabbin dabarun magance matsaloli, da ta kan yi ka'in da na'in, kuma ta kan yi gyare-gyare kan abubuwa da kanta, kana al'ummomin kasar Sin su ma suna kokari matuka kan ayyukansu da dai sauransu. Amma sun yi watsi da wani abu, wato kasar Sin da al'ummominta suna da niyya da karfi na yin kokarin cimma burinsu na neman ci gaba bisa shiri guda da suka tsara ba tare da jinkiri ba, wannan ya sa kasar Sin ta iya daukar matakan da suka dace kamar yadda ya kamata ba tare da tangarda ba a yayin aiwatar da manufar yin gyare-gyare a gida da bude kofarta ga waje.

Kasar Sin ta fara yin gyare-gyare da bude kofarta ga waje a yankunan kauyuka. Yau shekaru 40 da suka gabata, a asirce wasu manoma 18 na kauyen Xiaogang dake lardin Anhui suka kudiri aniyyar raba gonakin kauyensu ga kowane magidanci, ta yadda kowane magidanci zai noma shinkafa ko alkama da kansa, bayan sun girbe amfanin gona, sun mika wasu amfanin gona ga hukumar gwamnati bisa doka, sannan kowane magidanci zai yi amfani da ragowar, ta yadda za a samu abincin da kowane iyali zai ci. Nan da nan, aka fara yada wannan tsari da ake kira "samar da amfanin gona ta hanyar shuke-shuken da aka samu" a yankuna daban daban na fadin kasar Sin. Sakamakon haka, har yanzu ana ci gaba da bullo da karin matakan yin gyare-gayre kan harkokin da suka shafi aikin gona da harkokin kauyuka da kuma na manoma. Daga shekarar 1982 zuwa 2018, duk wata takarda da kwamitin kolin jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin ta fitar a farkon kowace shekara, tabbas ta shafi yadda za a yi gyare-gyare ko neman ci gaban yankunan karkara. A cikin farko shekaru 5 bayan shekarar 1982, kwamitin kolin JKS yana mai da hankali ne kawai kan yadda za a mika wa manoma ikon tafiyar da aikin gona da kansu, sannan a cikin shekaru 9 a jere, ta kan fitar da takardu, inda take mai da hankali kan yadda za a bunkasa yankunan karkara kamar yadda ake bunkasa birane tare. Yanzu, kwamitin kolin JKS ya fara mai da hankali kan yadda za a dauki lokaci mai tsawo ana gina yankunan karkara na zamani bisa manyan tsare-tsare a sabon yanayin da ake ciki yanzu. Babbar manufar da gwamnatin kasar Sin take aiwatarwa ita ce, bunkasa sana'o'i iri iri a kauyuka, inganta yanayin yankunan karkara, kyautata rayuwar al'ummomin kauyuka, tafiyar da harkokin kauyuka bisa doka, sannan dukkan manoma za su samu wadata.

Kasar Sin ta fara bude kofarta a garin Shenzhen na lardin Guangdong. Lamarin da ya sa yankuna daban daban na kasar Sin suka fara bude kofofinsu daya bayan daya ga ketare.

An fara inganta kayayyakin da 'yan kasuwa na kasashen waje suka shigo da su, da sarrafa kayayyakin masana'antu, zuwa yadda aka mai da wadannan biranen kasar Sin cibiyoyin kirkiro fasahohi masu ci gaba na duniya a yanzu. Muna iya cewa biranen Shenzhen da Shanghai da dai sauransu, sun taimakawa gyare-gyaren da ake yi a kasar, musamman a fannonin tattalin arziki da tsara birane. Bayan da Xi Jinping ya zama babban sakataren kwamitin tsakiya na jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin (JKS), ya zabi Shenzhen don ya zama birnin farko da ya kai ziyara. A wajen birnin, Xi ya tabo maganar da marigayi Deng Xiaoping ya yi, inda ya ce ya kamata a sabunta tunani, da nuna karfin hali wajen gwada sabbin dabaru. Ya ce, a nan gaba kasar Sin za ta ci gaba da bin madaidaiciyar hanyar da ta zaba, kuma za ta ci gaba da neman sabbin fasahohi da ci gaba. Sa'an nan a kwanan baya, shugaba Xi Jinping ya sake kai rangadi birnin Shenzhen, inda ya bayyana cewa, "Ba za a taba dakatar da manufar yin gyare-gyare da bude kofa a kasar Sin ba! Kuma kasar za ta nuna wa duniya wasu sabbin nasarori masu burgewa da za ta samu cikin shekaru 40 masu zuwa!"

Gyare-gyare a kauyuka, da wanda ake gudanarwa a birane, manyan fannoni ne guda 2 na matakan gyare-gyare da bude kofa na kasar Sin. Wadannan fannoni, sun hada da gyaran fuskar da ake yi a sauran fannoni na kasar, sun kuma zama cikakkun nasarorin da aka samu bisa aiwatar da manufar gyare-gyare da bude kofa cikin shekaru 40 da suka wuce. Tsakanin wannan lokaci, gwamnatin kasar Sin ta yi amfani da shirinta na raya kasa na shekaru biyar-biyar wajen tanadar ayyukan da za a gudanar wajen raya tattalin arziki da zaman al'umma, da sanya gyare-gyaren da ake yi a kasar bisa turba, ta yadda ba zai karkata zuwa wani gefe ba, sannan al'ummun kasar na dada samun biyan bukatu da gamsuwa. A wajen watan Oktoban bara, an tabbatar a yayin taron wakilan jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin karo na 19 cewa, kasar Sin za ta kafa wata al'umma mai walwala nan da shekarar 2020, sa'an nan za ta zamanintar da dukkan fannonin kasar bisa tsarin gurguzu zuwa shekarar 2035. Ban da haka, tana da burin zama wata babbar kasa mai karfi dake bin tsarin gurguzu, wanda ke samun wadata, da cikakken tsarin dimokuradiyya, da ci gaban al'adu, da jituwar zaman al'umma, zuwa tsakiyar karnin da muke ciki, wato dab da shekarar 2050.

Mene ne dalilin da ya sa kasar Sin ta yi nasarar kubutar da tattalin arzikinta daga bakin rushewa, sa'an nan ta raya kanta har ta zama kasa mafi karfin tattalin arziki ta biyu a duniya, duk cikin shekaru 40 da suka wuce? To, idan aka kalli wannan tambaya, za a iya fahimtar cewa, kasar Sin ta nuna cikakkiyar jajircewa a kokarinta na raya kasa bisa shirin da ta tsara, ko a fannin gyare-gyaren da ake yi a kauyuka, ko kuma a fannin raya birane, ma'anar ita ce tsayawa kan manufar gyare-gyare da bude kofa ba tare da kasala ba.

Kasar Sin tana tsayawa tsayin daka wajen aiwatar da manufar yin kwaskwarima a gida da bude kofa ga waje, kuma tana dukufa wajen aiwatar da wannan manufa domin cimma burinta da kuma bauta wa al'ummominta. Gwamnatin Sin ta kan inganta ayyukanta bisa bukatu da kuma fatan jama'ar kasa. Kamar yadda shugaba Xi Jinping ya bayyana, kasar Sin tana ci gaba da daukar matakan raya kasa, kana, duk wata matsalar da ta gamu da ita, ba za ta taba dakatar da ayyukan yin kwaskwarima a gida da bude kofa ga waje ba. Ya zuwa yanzu, an shiga muhimmin lokacin yin kwaskwarima a gida da bude kofa ga waje, ya kamata kasar Sin ta ci gaba da dukufa wajen warware dukkanin kalubalolin dake gabanta domin samun sabbin damammakin neman ci gaba.

Duk wata kasa na ganin cewa, yin kwaskwarima wani yaki mai nauyi kuma na dogon lokaci. Manufar yin kwaskwarima a gida da bude kofa ga waje ta dade a nan kasar Sin har kusan tsawon shekaru 40, dalilin da ya sa haka shi ne, manufar ta dace da yanayin kasar Sin, kuma lalle al'ummomin kasar Sin na ganin cewa, wannan wata sa'a ce, musamman ma a wannan lokacin da ake fuskantar kalubaloli da dama a fadin duniya. Wasu kasashen duniya sun shiga wani mawuyacin halin neman ci gaba, sabo da canjin manufofin neman bunkasuwar kasa a yayin da aka samu sauyin shugabanci. Amma, ana ci gaba da bin hanya daya wajen neman bunkasuwar Sin, lamarin da kuma ya tabbatar da yanayin zaman karko na karuwar tattalin arzikin duniya. (Masu Fassarawa: Sanusi Chen, Bello Wang, Maryam Yang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China