A jawabin da ya gabatar yayin taron, shugaba Xi ya zayyana ayyukan tattalin arzikin kasar Sin a shekarar 2018, sannan ya yi tsokaci kan yanayin da tattalin arzikin duniya ke ciki, kana ya gabatar da shirin ayyukan da za a gudanar a shekara mai zuwa.
Shugabannin kasar Sin da suka halarci taron sun tabbatar da wasu manyan ayyukan da za a lura da su a shekarar 2019, wadanda suka hada da: raya masana'antu mai inganci, da habaka kasuwannin cikin gida, da raya kauyuka da yankunan karkara, da neman samun daidaito tsakanin shiyyoyi daban daban, da kara kokarin gyara tsarin tattalin arziki, da bude kofa ga kasashen waje daga dukkan fannoni, gami da kara kyautata zaman rayuwar jama'ar kasar. (Bello Wang)