A yau Jumma'a, yayin wani taron manema labaru da ya gudana a birnin Beijing, fadar mulkin kasar ta Sin, madam Hua Chunying, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin, ta karyata wani labarin da gidan rediyon muryar Amurka VOA ya watsa, cewa wai "bankin duniya ya shawarci kasar Sin don ta gyara manufar cinikinta na rashin daidaito". Jami'ar kasar Sin ta jaddada nacewar kasar Sin kan manufar bude kofa da ciniki cikin 'yanci, gami da kare tsarin ciniki na neman biyan bukatun bangarori daban daban. Ta kara da cewa, kasar Sin ba ta da niyyar takaddama da wata kasa a fannin ciniki.
Haka kuma, Madam Hua ta ce, kasar Sin ta yarda da kalaman da shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya fada, inda ya nuna yabo kan nasarorin da kasar Sin ta samu albarkacin manufarta ta yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga kasashen waje, da kuma kyakkyawar huldar dake tsakanin kasashen Sin da Rasha. A cewar ta, kasar Sin kasa ce dake son hada kai tare da bangaren Rasha, don habaka hadin gwiwar kasashen 2 a fannoni daban daban. (Bello Wang)