Kudurin dai ya bayyana cewa, kaso kusan 80 bisa dari na masu fama da kangin talauci, na zaune ne a yankunan karkara, inda suke dogaro da noma domin ciyar da kan su. Don haka aka sanya batun yaki da fatara a sahun gaba cikin ajandar ci gaba mai dorewa ta MDD nan da shekarar 2030.
Sannan yaki da fatarar a cewar kudurin, sun hada da daukar matakan bunkasa samar da ababen more rayuwa, da samar da kudaden aiwatar da tsare tsare, da samar da guraben ayyukan yi, da raya ilimi, da tsarin inganta zamantakewar al'umma, tare da rage gibi a fannin amfani da na'urorin zamani don inganta rayuwa.
Bayan amincewa da kuduri, wakilin Sin a MDD Ma Zhaoxu, ya shaidawa manema labarai cewa, Sin da kungiyar G77, na da nufin karfafa gwiwar kasashen duniya su yi aiki tare, wajen kawar da talauci tsakanin al'ummun karkara, da aiwatar da ajandar 2030 yadda ya kamata.(Saminu Alhassan)