in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Amurka ta sanya takunkumi kan mutanen Rasha 18 da kamfanoni 4
2018-12-21 10:53:37 cri

A ranar Laraba gwamnatin Amurka ta sanar da cewa, ta kakaba takunkumi kan mutane 18 'yan kasar Rasha da kuma wasu kamfanoni kasar 4, in ji wata sanarwa daga ma'aikatar kudaden kasar Amurkar.

Sanarwar ta ce, an dauki wannan mataki ne domin maidawa Rasha martani dangane da yadda take ci gaba da rashin mutunta dokokin kasa da kasa.

A cewar sanarwar, mutane 15 daga cikin 18, mambobi ne na hukumar leken asirin kasar Rashar (GRU), wanda Amurkar ke zargin su da hannu wajen yunkurin yin katsalandan a harkokin zaben Amurka a shekarar 2016, a yunkurin yin zagon kasa ga kungiyoyin kasa da kasa ta hanyar yin kutse ta tashar yanar gizo, kana da yunkurin yin kisan gilla a kasar Birtaniya.

Amurka ta kuma sanya takunkumi kan wasu kamfanoni 4 da wasu mutane da dama 'yan kasar Rasha a yunkurinsu na yin shisshigi game da harkokin siyasa da tsarin zabuka na kasashen duniya, in ji sanarwar.

Dukkan wasu kaddarori ko kuma ribar da aka samu daga dukiyoyin da wadannan mutanen suka mallaka wadanda ke karkashin hurumin Amurka an toshe su, kuma Amurkar ta haramtawa kanta yin duk wata huldar ciniki da mutanen, in ji sanarwar.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China