in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jakadan MDD bai ce uffan ba game da janyewar dakarun Amurka daga Syria
2018-12-21 10:06:50 cri

Wakilin musamman na MDD game da batun kasar Syria Staffan de Mistura bai nuna sha'awar yin tsokaci ba game da matakin da shugaban Amurka Donald Trump ya dauka na janye dakarun Amurkar daga Syria.

"Daga bangare na a yanzu haka tamkar yin gaggawa ne na yi wani tsokaci dangane da batu mai cike da sarkakiya, wannan muhimmin matakin, wanda aka sanar da shi a jiya, a dukkan bangarorin wato bangaren siyasa da bangaren soji," de Mistura ya bayyana hakan ne ga manema labarai bayan jawabin da ya gabatarwa kwamitin sulhun MDD.

A ranar Laraba ne fadar White House ta sanar da cewa, gwamnatin Trump ta fara janye dakarun Amurka daga Syria, bayan da aka sanar da cewa an samu nasara a yakin da ake yi da mayakan kungiyar 'yan ta'adda na IS a yankin.

Da aka tambaye shi tun a jiya Alhamis, yayin da aka nemi ya yi tsokaci game da matakin da Amurka ta dauka, jakadan Faransa a MDD Francois Delattre ya ce: "Muna da matukar bukatar manufofin siyasar Amurka wajen warware rikicin siyasar kasar Syria."(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China