in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sharhi: Dole ne kasar Sin ta kara bude kofa don samun ci gaba mai inganci
2018-12-20 21:54:25 cri

A yayin bikin da aka gudanar a birnin Beijing na kasar Sin don murnar cika shekaru 40 da fara aiwatar da manufar gyare-gyare a cikin gida da bude kofa ga kasashen waje a kasar Sin, shugaban kasar Xi Jinping ya zayyana wasu muhimman dabaru guda 9 da kasar ta samu yayin aiwatar da manufar, kuma daya daga cikinsu shi ne: Dole ne kasar Sin ta kara kokarin bude kofarta, da neman kafa kyakkyawar makoma ta bai daya ga daukacin al'umma. Wannan dabara tana da ma'anar musamman ta kuma yi wa kasar jagora a yunkurin raya tattalin arzikinta, da tabbatar ma ingancinsa.

A shekaru 40 baya, kasar Sin ba ta bude kofarta sosai ba tukuna, kana yawan matsayin cinikinta yana matsayi na 29 a duniya. Sa'an nan daga watan Disamban shekarar 1978, jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin dake rike da ragamar mulkin kasar ta tsai da kudurin sauya manufarta, inda ta fara mai da cikakken hankali kan raya tattalin arziki. Daga bisani sai aka fara aiwatar da manufar yin gyare-gyare da bude kofa, don shigo da sabbin fasahohi, wadanda suka taimaka wajen raya tattalin arzikin kasar matuka.

Cikin wadannan shekaru 40 da suka gabata, kasar Sin ta kebe wani yankin ciniki na musamman, da sanya aka bude kofa a biranen dake bakin teku, da koguna, da wadanda ke dab da layin dogo, da kuma tsakiyar kasar. Ban da haka kuma, kasar ta shiga kungiyar ciniki ta duniya WTO, ta kuma gabatar da shawarar "Ziri Daya da Hanya Daya". Haka zalika, ta kafa wasu yankunan ciniki cikin 'yanci na gwaji guda 12, da tsara bude tashar ciniki cikin 'yanci mai halayyar musamman ta kasar Sin. Ta wadannan matakai, tsarin bude kofa na kasar ya kunshi fannoni daban daban, ya kuma sanya kasar ta zama ta farko a duniya ta fuskar yawan ciniki, da kawar ciniki mafi girma ta kasashe da yankuna fiye da 120, kuma ta biyu a duniya a fannin shigo da jarin waje da zuba jari kai tsaye ga kasashen waje. Ma'aunin tattalin arziki na GDPn kasar Sin a shekarar 2017 ya ninka na shekarar 1978 har sau 33.5, wato karuwar kimanin kashi 9.5% a duk shekara, wata karuwar da ta wuce matsakaicin karuwar tattalin arzikin duniya ta kashi 2.9% sosai, lamarin da al'ummomin kasashen duniya ke kallo a matsayin abin al'ajabi. Dangane da wannan batu, shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya takaita cewa, "bude kofa ya sa an samu ci gaba, yayin da rufe kofa zai haddasa koma baya."

Duk da haka, mun san cewa, idan ana son kwatanta ci gaban tattalin arzikin wata kasa, bai kamata ba a lura da karuwar ma'aunin tattalin arziki kawai, maimakon haka sai a yi la'akari da wasu fannoni daban daban. Alal misali, a fannin samun kayayyakin na'urori na amfanin gida. A shekarun 1980, Sinawa su kan yi alfahari idan suna da na'urorin talabijin da na'urorin sanyaya kayan abinci da na wanke tufafi a gidjensu. Amma zuwa yanzu, an fi son samun kayayyakin da za su inganta zaman rayuwarsu, irinsu na'urar wanke kwano, da injin tsabtace ruwan sha, da mutum-mutumin tsabtace gida dake sarrafa kansa, da dai makamantansu. Wannan ci gaban ya tabbatar da gaskiyar wani ra'ayin da aka bayyana a wajen babban taron wakilan jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin karon 19, wato bukatun Sinawa a fannin kyautata rayuwarsu na dada daga matsayinsu, haka kuma ya nuna cewa, tattalin arziki ya bar bunkasa cikin sauri, ya karkata ga samun inganci.

Wannan shi ne sakamakon da tabbas za a samu a lokacin da kasar Sin ta shiga sabon lokaci bayan da ta shafe shekaru 40 tana aiwatar da manufar yin gyare-gyare a gida da bude kofarta ga waje. A lokacin da yake amsa tambayar da aka yi masa game da yadda za a cimma wannan burin, shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya ba da tabbaci cewa, tattalin arzikin kasar Sin ya samu bunkasa ne sakamakon aiwatar da manufar bude kofarta ga waje, sakamakon haka, tabbas kasar Sin za ta bunkasa tattalin arziki mai inganci bisa manufar kara bude kofarta ga waje.

Masu fashin baki na nuna cewa, a shekarar bana, kalmar "bude kofa" ta kan fito daga bakin shugabannin kasar Sin. A tarukan ko bukukuwa na kasa da kasa manya ko kanana, sau da dama, shugaba Xi Jinping yana sanar da sauran kasashen duniya wani labari da ya dace a bayyane, wato tabbas "kasar Sin ba za ta dakatar da manufarta ta bude kofa ba har abada". A cikin watannin da suka gabata, yawan kudin haraji da hukumar kwastam ta kasar Sin ta sanya kan hajojin kasashen waje ya ragu zuwa 7.5%, ta kuma kara bude kasuwannin hada-hadar kudi da kera motoci da jiragen sama da kuma jiragen ruwa ga jarin waje. Jimillar kwangilolin da aka daddale a farkon bikin baje kolin kayayyakin da ake shigo da su kasar Sin daga kasashen waje ta kai dalar Amurka biliyan 57.8, a cikin wani rahoton da bankin duniya ya fitar game da yadda kasashen duniya suke kyautata yanayin kasuwanci a cikin shekara daya da ta gabata, matsayin kasar Sin a wannan fanni ya karu fiye da 30……Baya ga niyyar kasar Sin, har ma ta riga ta dauki matakan bude kasuwarta ga duk duniya. Peter Drysdale, shehun malami a fannin ilmin tattalin arziki, kuma shugaban hukumar nazarin tattalin arzikin gabashin Asiya ta jami'ar kasar Australiya ya yi sharhi cewa, tabbas kasar Sin za ta ci gaba da aiwatar da manufarta ta bude kofarta har abada.

Ko shakka babu, a yayin da kasar Sin take kara bude kofarta ga ketare, tabbas a lokacin da ta samu yabo da damammaki, za kuma ta tinkari kalubaloli iri iri. Yanzu fasahohin zamani da sauyin salon bunkasa masana'antu na hanzarta samun ci gaba a duk fadin duniya, sakamakon haka, za a bullo da dimbin fasahohin zamani da sabbin masana'antu da kuma sabbin salon neman ci gaba, tabbas za su zama muhimmin karfin da kasar Sin za ta iya yin amfani da shi wajen kyautata tsarin bunkasa tattalin arzikinta, da kuma yin watsi da tsoffin masana'antun da ba su yi daidai da zamanin da ake ciki ba.

Wannan wata dama ce ta samu yabo da damammaki ga kasar, amma a wani bangare na daban, yanzu matakan ba da kariya ga harkokin cinikayya da daukar matakai na kashin kai da kuma rigingimun cinikayya tsakanin kasa da kasa sun tsananta, kuma wadannan za su kawo wa kasar Sin karin kalubaloli da yanayi na rashin tabbas.

Batun tambayar "Ko kara bude kofa ko rufe kofa, ko neman karin ci gaba ko kuma koma baya" da aka haddasa mata, shugabanni da al'ummomin kasar Sin sun ba da amsa da kakkausar murya, cewar kasar Sin ba za ta fuskanci koma baya ko kadan ba! Kuma za ta kara bude kofarta ga duk duniya maimakon rufe ta.

Cikin jawabinsa, shugaba Xi ya bayyana cewa, shirin "Ziri daya da hanya daya" zai kasance muhimmin dandalin neman bunkasuwar kasar ta Sin, kuma manyan ka'idojin da za a bi wajen gudanar da wannan shiri su ne yin shawarwari tare, gudanar da shirin tare da kuma cimma nasara tare. Sin tana son hada kai da kasa da kasa domin gudanar da wannan shiri cikin hadin gwiwa, ta yadda zai kasance wani muhimmin dandalin neman ci gaba na bangarori daban daban da abin ya shafa. Cikin shekaru 5 da suka gabata, darajar cinikin dake tsakanin kasar Sin da kasashen da suke cikin shirin "Ziri daya da hanya daya" ya wuce dallar Amurka biliyan dubu 5, kuma adadin jarin da ta zuba kai tsaye a kasashen ketare ya wuce dallar Amurka biliyan 60, ta kuma samar da guraben aikin yi a kasashe sama da dubu dari 2. Shi ya sa, gudanar da shirin "Ziri daya da hanya daya" cikin hadin gwiwa ya dace da bunkatun kasa da kasa na neman ci gaba, ya kuma dace da burin kasar Sin na yin kwaskwarima a gida da bude kofa ga waje da kuma karfafa dunkulewar kasa da kasa.

A watan Agusta na shekarar bana, shugaba Xi ya bayyana a yayin taron murnar cika shekaru 5 da inganta shirin "Ziri daya da hanya daya" cewa, ya kamata mu hada shirin da sauran manufofin raya kasa na Sin, domin habaka hadin gwiwarmu wajen raya kasar Sin a fannoni daban daban. Lamarin da ya nuna cewa, dandalin "Ziri daya da hanya daya" zai ba da gudummawa kan bunkasuwar kasar Sin yadda ya kamata, da kuma karfafa ayyukan yin kwaskwarima a gida da bude kofa ga waje, da baiwa kasar Sin dama wajen ba da sabuwar gudummawa ga bunkasuwar kasashen duniya baki daya.

Al'ummomin kasashen duniya za su gane cewa, kasar Sin tana kara bude kofa ga waje, ci gaba da inganta tsarin tattalin arzikin kasa da kasa, da kuma dukufa wajen karfafa dunkulewar dukkanin bil Adama, kamar yadda shugaba Xi Jinping ya bayyana. (Sanusi Chen, Bello Wang, Maryam Yang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China