in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Karuwar cinikin kasar Sin tana taka muhimmiyar rawa ga ci gaban cinikin duniya
2018-12-20 19:13:57 cri
Zou Zhiwu, mataimakin babban darektan hukumar kwastam ta kasar Sin, ya furta a yau Alhamis cewa, tun bayan kaddamar da manufar gyare-gyare a gida da bude kofa ga kasashen waje a kasar Sin shekaru 40 da suka wuce, yawan kudin kayayyakin shigi da fici na kasar a shekara ya ninka har sau 198, wanda ya zarce kashi 11% na yawan cinikin da ake yi a duniya, kana karuwar da kasar Sin ta samu a fannin ciniki ta taka muhimmiyar rawa ga ci gaban cinikayyar duniya.

Jami'in ya kara da cewa, albarkacin manufar kasar Sin na yin gyare-gyare da bude kofa, al'ummun kasashe daban-daban na kallon karuwar cinikin da kasar Sin take yi da kasashen waje kamar wani abin al'ajabi, inda matsakacin karuwar da a kan samu a kowace shekara ta kai kimanin 14.5%. (Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China