in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Babban taron MDD ya zartas da yarjejeniyar kaurar jama'a tsakanin kasa da kasa
2018-12-20 15:49:21 cri

Jiya Laraba babban taron MDD ya zartas da yarjejeniyar kaurar jama'a tsakanin kasa da kasa a fadin duniya a hukumance. Game da hakan, babban sakataren MDD Antonio Guterres ya fitar da wata sanarwa, inda ya bayyana cewa, yarjejeniyar da aka zartas, za ta samar da wani dandalin hadin gwiwa dake tsakanin kasa da kasa a fannin kaurar jama'a.

A wannan rana, babban taron MDD ya zartas da yarjejeniyar ne bisa kuri'un amincewa 152, da na adawa 5, da kuma na janye jiki guda 12. Kasashen Amurka, da Isra'ila, da Czech, da Hungary da Poland, sun jefa kuri'un adawa, kana wasu kasashe mambobin MDD 24 ba su shiga taron ba.

Yarjejeniyar da aka zartas, ita ce irin ta ta farko tsakanin gwamnatocin kasashen duniya a fannin kaurar jama'a tsakanin kasa da kasa, an kuma shafe watanni 18 ana tsara ta. Ya zuwa ranar 23 ga watan Yulin bana, kasashe mambobin MDD ban da Amurka, sun cimma matsaya guda kan batun, amma yarjejeniyar ba ta da kariya ta fuskar doka.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China