in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sharhi: Shaida yadda aka yi gyare-gyare da bude kofa a kasar Sin
2018-12-19 21:07:30 cri

Manufar gyare-gyare a gida da bude kofa ga kasashen waje da aka kaddamar a shekarar 1978 a kasar Sin ta sauya yanayin da kasar take ciki, gami da samar da dimbin tasiri ga duniya. Kasar Sin, a matsayinta na kasar da ta kan nuna godiya, ba za ta manta da 'yan kasashen wajen da suka taba baiwa kasar goyon baya ba.

A jawabin da ya gabatar yayin taron murnar cika shekaru 40 da fara aiwatar da manufar gyare-gyare da bude kofa, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya nuna godiya ga 'yan kasashen waje da suka taba tallafawa kasar Sin yayin da take kokarin yin gyare-gyare da bude kofa, gami da zamanintar da al'umma. A yayin wannan taron ne kuma, aka karrama wasu baki 10 da lambar yabo ta "sada zumunta a fannin gyare-gyaren da kasar Sin take yi". Cikinsu, akwai Alain Merieux, wanda ya taba taimakawa kasar Sin yaki da cutar SARS da murar tsuntsaye; da Werner Gerich, shugaban ma'aikatar sarrafa kaya na farko da aka taba samu a tarihin kasar Sin; da Klaus Schwab, wanda ya ba da taimako ga kasar Sin bisa kokarinta na shiga cikin tsare-tsaren tattalin arzikin duniya; da Konosuke Matsushita, wanda ya taimaka wajen raya masana'antun kasar Sin, da dai makamantansu. Wadannan mutanen da suka samu wannan kyauta, suna gudanar da sana'o'in da suka hada da aikin jinya, da samar da kaya, da wasannin motsa jiki, da siyasa, da tattalin arziki, da dai sauransu. Amma ma iya ce suna da wani take guda daya, wato wadanda suka shaida yadda kasar Sin take aiwatar da manufar gyare-gyare da bude kofa, gami da samar da gudummawa a wannan kokarin da ake yi.

Lokacin da kasar Sin ta yanke shawarar daukar matakan gyare-gyare da bude kofa, tattalin arzkinta na dab da rushewa, kana dukkan fannonin kasar na bukatar gyaran fuska. A sa'i daya, kimiyya da fasaha, da tattalin arziki na samun ci gaba cikin sauri, a sauran kasashe daban daban na duniyarmu. Saboda haka, kasar Sin a lokacin tana kishin samun damar koyon fasahohi na sauran kasashe, da shigar da kwararru cikin kasar.

Bayan aka fara aiwatar da manufar yin kwaskwarima a gida da bude kofa ga waje, kasar Sin ta gayyaci kwararre a fannin tafiyar da harkokin kasuwanci na kasar Jamus Werner Gerich da ya zo kasar Sin, domin zama shugaban masana'antar kera injuna masu aiki da man dizal ta Wuhan. Mr. Gerich ya tafiyar da harkokin masana'antar bisa ka'idojin tabbatar da ingancin injuna da kuma mai da hankali kan bukatun kasuwanci. Lamarin da ya sa, masana'antar ta fara fitar da injuna zuwa kasashe guda 7 dake yankin kudu maso gabashin Asiya, ya kuma yi tasiri kan yadda kamfanonin kasar Sin suka gudanar da ayyukansu.

Haka kuma, a lokacin da yake rike da mukamin firaministan kasar Singapore Lee Kuan Yew ya dukufa wajen kafa yankin masana'antu na Sin da Singapore dake birnin Suzhou, yankin kwaskwarima na gwaji a kasar Sin, da kuma abin koyi na hadin gwiwar kasa da kasa. Haka kuma, ra'ayinsa na "kowa na da wurin zama" da shirin "samar da gidaje masu araha" da ya gabatar, sun taimakawa kasar Sin wajen warware matsalar karancin gidajen kwana da take fuskanta.

A hakika dai, akwai 'yan kasashen waje masu dimbin yawa da suka taba ba da taimako ga kasar Sin a yayin da take aiwatar da manufar yin kwaskwarima a gida da kuma bude kofa ga waje. Wadannan mutane guda 10 da suka lashe lambar yabo sun zama alama ta ci gaban kasar Sin da kuma yadda kasar Sin take yin kwaskwarima a gida domin hada kan kasashen duniya. Kuma wadannan 'yan kasashen waje sun ba da babbar gudummawa ga ci gaban kasar Sin, Sinawa ba za su manta da su ba.

A sa'i daya kuma, kasar Sin ta samar da damammaki masu kyau ga kasashen duniya, kamfanonin ketare da dama sun sami sabuwar karuwa sabo da manyan kasuwanni a kasar Sin. Kuma, Sin ta ba da gudummawa na kaso 30 cikin 100 ga bunkasuwar tattalin arzikin duniya cikin shekaru da dama da suka gabata. Bugu da kari, tsakanin shekarar 2013 zuwa shekarar 2017, kasar Sin ta samar da guraben aikin yi sama da dubu dari 20 a yankunan hadin gwiwar ciniki dake kasashen dake cikin shirin "Ziri daya da hanya daya".

Bayan shekarar 2004, jimillar yawan taimakon jin kai da kasar Sin ta baiwa sauran kasashen duniya ya zarce 300, wato matsakaicin yawan karuwarsu ya kai 29.4%. A lokacin da take kokarin shiga ayyukan shimfida zaman lafiya na MDD, kasar Sin ta kuma soke basusukan da yawansu ya kai fiye da dalar Amurka biliyan gomai da ta baiwa kasashe masu fama da talauci, sannan ta samar wa kasashen Afirka kudin neman ci gaba har dalar Amurka a kalla biliyan 60, a yayin da ta horar da dubban daruruwan kwararru na wasu kasashe masu tasowa. Kamar yadda ya bayyana a cikin jawabinsa, Shugaba Xi Jinping ya ce, yanzu kasar Sin tana shiga tsakiyar dandali na duniya a kai a kai, "kamar yadda sauran kasashen duniya suke amincewa, yanzu kasar Sin ta kuma zama mai tabbatar da zaman lafiyar duniya, kana mai bayar da gudummawa ga ci gaban duk duniya baki daya, kuma wadda ke kokarin tabbatar da tsarin tafiyar da harkokin duniya na yanzu."

Yanzu, kasar Sin za ta kara yin gyare-gyare a gida da bude kofarta ga ketare bisa sakamakon da ta samu yanzu. Kasar Sin ta kasance kamar wata babbar kasuwa ce dake da mutane biliyan 1.4, inda kowa ke kokarin kirkiro sabbin fasahohin zamani, da kuma kyautata yanayin kasuwanci…… Sannan kasar Sin za ta samar wa kamfanoin jarin waje da 'yan kasashen waje karin damammaki da fannoni na neman ci gaba fiye da yadda ta taba bayarwa cikin shekaru 40 da suka gabata. Yadda ya gani da idanunsu da yadda ya halarta da kuma yadda zai ci gajiyar sabon sakamakon yin gyare-gyare da bude kofa da kasar Sin za ta samu, za su zama damar da bai kamata kowane bako ko kamfani mai jarin waje su yi watsi da ita ba. (Sanusi Chen, Bello Wang, Maryam Yang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China