in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Rasha da Iran da Turkiyya sun amince da kiran taron farko na kwamitin tsara kundin mulkin Syria
2018-12-19 11:05:54 cri

Kasashen Rasha, da Iran, da Turkiyya, sun amince da kiran taron farko, na kwamitin da zai tsara kundin mulkin kasar Syria a farkon shekarar 2019 dake tafe.

Cikin wata sanarwar hadin gwiwa da aka sanyawa hannu a jiya, bayan kammala taron ministocin kasashen, da wakilin musamman na MDD game da batun kasar ta Syria Staffan de Mistura, daukacin wakilan kasashen sun amince cewa, kwamitin zai gudanar da ayyukan sa bisa sanin ya kamata, da sanya kwazo wajen cimma nasarar da ake fata.

Bayan kammalar ganawar manyan jami'an, wakilin na MDD ya kuma gana da manema labarai, inda ya bayyana cewa, ganawar sa da manistocin harkokin wajen kasashen masu muhimmanci uku, bangare ne na burin da ake da shi, game da kafa kwamiti mai nagarta na Syria, wanda kuma Syria za ta jagoranta, kana MDD ta tallafawa ayyukan sa.

To sai dai kuma Staffan de Mistura ya ce, akwai sauran rina a kaba game da fatan kafuwar wannan muhimmin kwamiti, wanda zai zamo mai cike da adalci da daidaito. Ya kuma bayyana shirin sa na kara tuntubar babban magatakardar MDD a birnin New York, kana zai yiwa kwamitin tsaron majalissar karin haske game da halin da ake ciki a gobe Alhamis.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China