Irin aikin da Japan ta yi ba shi da amfani wajen kyautatawa da kuma ci gaban dangantakar dake tsakanin Sin da Japan, kuma ba ya amfani a fannin zaman lafiya da zaman karko na shiyyar. Kasar Sin ta nuna rashin jin dadi da adawa kan haka, kuma ta riga ta nuna matukar takaici game da haka.
Baya ga haka, Hua ta nuna cewa, sakamakon wasu dalilan tarihi ne, kullum ayyukan da Japan ta dauka a fannin tsaron aikin soja ke jawo hankula sosai daga kasashe makwabtan ta, da ma sauran kasashen duniya. Don haka, kasar Sin ta kalubalanci Japan da ta cika alkawarinta na bin manufar kai farmaki kadai idan an kai mata farmaki, da tsayawa kan hanyar samun ci gaba cikin lumana, da yin taka tsantsan a fannin tsaron aikin soja. (Bilkisu)