Masu binciken kimiyya na kasar Sin sun gano wani bigire da zai dace da gina filin tashi da saukar jiragen sama a yankin Antarctic mai tsananin sanyi.
Wannan wuri dai na da nisan kilomita 10 daga tashar bincike da masanan na Sin suka kafa a yankin karshen kusurwar kudancin yankin.
Da yake tsokaci game da hakan, jagoran tawagar Sin dake bincike a yankin na Antarctic Sun Bo, ya ce wurin zai iya samar da damar sauka da tashin ko wane nau'i na jirgin sama.
A yanzu haka dai akwai irin wadannan bigire dake dacewa da ginin filin jirgin sama a yankin karshen kusurwar kudancin yankin na Antarctic har guda 8, amma Sin ba ta kai ga gina filin saukar jirage na kashin kan ta ba tukuna.