Shugaban na Sudan ya samu tarba daga takwaransa na Syria Bashar al-Assad a filin jirgin saman kasa da kasa na Damascus, in ji kamfanin dillancin labaran SANA.
Al-Bashir ya isa birnin Damascus ne domin ziyarar aiki.
A lokacin ganawarsu, shugabannin biyu sun cimma matsaya cewa, tashe tashen hankulan dake addabar mafi yawan kasashen larabawa yana bukatar a dauki sabbin matakai wajen dakile shi ta hanyar mutunta ikon kasa da kuma bin tsarin kaucewa yin shisshigi a harkokin ikon kasashen.
Al-Bashir, ya yi fatan za'a samu kyautatuwar al'amurra a Syria hanzari, kana yana fatan al'ummar kasar zasu nemawa kasarsu makoma ba tare da yin katsalandan daga kasashen waje ba.
Shugaban na Sudan ya kuma bayyana goyon bayan kasarsa ga Syria, yana mai cewa Sudan a shirye take ta bayar da dukkan goyon bayan da ake bukata wajen tabbatar da kare ikon kasar Syria da kuma tabbatar da hadin kan kasar.
A nasa banfaren, Assad yace, ziyarar ta al-Bashir zata bada kwarin gwiwa wajen kyautata dangantakar dake tsakanin kasashen biyu kamar yadda take a baya gabanin aukuwar rikici a kasar.