in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Syria da Iran sun tattauna yadda za'a kafa kwamitin shirya kundin tsarin mulkin Syrian
2018-12-17 10:46:58 cri
Shugaban kasar Syria Bashar al-Assad a jiya Lahadi ya gana da jami'in kasar Iran wanda ke ziyarar aiki a kasar inda suka tattauna game da yadda za'a kafa kwamitin da zai jagoranci shirya kundin tsarin mulkin kasar Syrian, kamar yadda ofishin yada labaran shugaban kasar ya sanar da hakan.

A lokacin ganawar, Hossein Jaberi Ansari, mataimaki na musamman mai kula da harkokin siyasa na ministan harkokin wajen kasar Iran, ya sanar da shugaba al-Assad game da shirye shiryen da ake yi na taron da za'a gudanar tsakanin Rasha, Iran da Turkiyya a birnin Geneva nan da wasu 'yan kwanaki masu zuwa, bayan yarjejeniyar da aka cimma game da tabbatar da tsarin karshe na kwamitin na shirya kundin tsarin mulkin kasar.

Ansari, ya bayyana aniyar kasar Iran na yin aiki tare da gwamnatin Syria wanda hakan ya bayyana babban sauyi game da cimma yarjejeniyar kafa kwamitin tsara kundin mulkin kasar ta Syria.

A nasa bangaren, Assad ya yaba da irin kokarin da Iran ke yi wajen tabbatar da kafa kwamitin tsara kundin mulkin duk da irin matsin lambar da ake fuskanta daga wasu kasashe dake taimakwa ayyukan ta'addanci.

Shugaban kasar ya kuma nanata irin kokarin da kasashen Rasha da Iran ke yi wajen hana kasashen yammacin duniya yin katsalandan game da batun dambarwar siyasar kasar Syrian ta hanyar goyon bayan da suke nunawa na kokarin warware rikicin kasar ta Syria ba tare da yin shisshigi daga kasashen waje ba. (Ahmad)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China