Masu zanga zangar suna bayyana adawarsu ne bisa yarjejeniyar makauratan wanda MDD ta sanyawa hannu a Marrakech a makon jiya, masu zanga-zangar sun nuna fargaba game da yarjejeniyar inda suke ganin zata iya haifar da yawaitar masu yin hijira.
Jami'an 'yan sanda sun yi amfani da hayaki mai sa hawaye da Motar fesa ruwa a lokacin arangama da masu zanga zangar a kusa da helkwatar kungiyar tarayyar Turai.
Rahotanni sun ce, sama da masu zanga zangar 5,500 ne suka yi dandazo daga bangarorin biyu.
Ofishin masu gabatar da kara a birnin Brussels sun tabbatar da cafke mutane dari daya.