in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Babban jami'in MDD ya bukaci a kyautata tsarin yin kaura na kasa da kasa
2018-12-16 16:15:02 cri
Sakatare janar na MDD Antonio Guterres, ya bayyana cewa, yin kaura tamkar wata hanya ce ta daga matsayin tattalin arziki, don haka ya bukaci a samar da kyakkyawan tsari game da batun tafiyar da al'amurran kaura na kasa da kasa.

A sakon da ya aike game da ranar da MDD ta kebe a matsayin Ranar Makaurata ta kasa da kasa wadda za'a gudanar a ranar 18 ga watan Disamba, misata Guterres ya fada a ranar Juma'a cewa, "yin hijira wata muhimmiyar hanya ce ta daga matsayin tattalin arziki, da kawo sauyi da fahimtar juna. Tana baiwa miliyoyin mutane sabbin damammaki, da amfanawa al'ummomi masu karbar bakuncin makaurata har ma ga kasashen masu yin kaurar na asali."

To sai dai kuma, ya yi gargadin cewa, muddin aka samar da dokoki marasa inganci, batun yin kaura zai iya haifar da rarrabuwar kawuna a tsakanin al'ummomi, zai haifar da cin zarafi da bautar da al'umma, kana zai iya haifar da koma baya ga sha'anin mulki.

Ya sake waiwayen game da batun amincewa da yarjejeniyar makaurata mai cike da tarihi wadda aka amince da ita a farkon wannan watan, ya ce an dauki wannan mataki ne bisa amincewar kasashe mambobin kwamitin MDD.

Babban jami'in MDD ya bayyana kyakkyawar fatansa cewa, yarjejeniyar za ta taimaka musu wajen tunkarar ainihin manyan kalubalolin dake shafar batun makaurata da kuma zakulo irin alfanun dake tattare da batun. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China