in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Babban taron sauyin yanayi na MDD ya fitar da jadawalin aiwatar da yarjejeniyar Paris
2018-12-16 15:43:39 cri
Masu shiga tsakani daga kasashen duniya kusan 200 a jiya Asabar sun cimma matsaya game da ka'idojin da za'a bi wajen aiwatar da yarjejeniyar sauyin yanayi wadda aka gabatar da ita a lokacin babban taron sauyin yanayin na birnin Paris a shekarar 2015.

Taron na masu ruwa da tsaki karo na 24 wato (COP 24) a takaice, wanda ya shafi batun aiwatar da yarjejeniyar MDDr game da batun sauyin yanayi (UNFCCC), taron ya zarta lokacin da aka dibar masa a hukumance wanda da farko aka shirya karkare taron da yammacin ranar Juma'a, amma ya tsallaka zuwa ranar Asabar wanda ya gudana a birnin Katowice dake kudancin kasar Poland.

"Wannan ba aiki ne mai sauki ba. Yana da matukar wahala da firgitarwa, amma duk da haka mun kammala shi," in ji Michal Kurtyka, shugaban taron na COP24 kana sakataren hukumar makamashin kasar Poland.

An bayyana taron na COP24 a matsayin taro mafi muhimmanci da ya gudana tun bayan babban taron sauyin yanayi na yarjejeniyar Paris a 2015, wanda a lokacin ne aka cimma matsaya na rage dumamar yanayin duniya da kasa da maki biyu a ma'aunin Celsius, yayin da ake ta kokarin kara kaimi na cimma nasarar rage maki 1.5 a ma'aunin Celsius 1.5 na dumamar yanayin duniya. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China