in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta yi gargadi game da rashin tabbas a ci gaban zaman lafiyar Yemen
2018-12-15 16:17:10 cri

Babban jami'in kula da shirin jin kan bil adama na MDD Mark Lowcock a jiya Juma'a ya yi gargadi game da rashin tabbas dangane batun shirin tattaunawar magance rikicin Yemen na MDD, ya bayyana cewa, har yanzu akwai babbar barazana da kasar ke iya fuskanta.

"Wannan mako nasarar da aka samu ba ta da tabbas, a zahiri ma kishiyar hakan ne aka samu. Dole ne a aiwatar da kudurori, wadanda za su taimaka wajen tabbatar da zaman lafiya. A tsawon lokaci, miliyoyin 'yan kasar Yemen har yanzu suna cikin matsananciyar bukatar tallafi da kuma ba su kariya," Lowcock ya fadawa kwamitin tsaron MDD, inda yake buga misali game da nasarar shirin MDD na shirya tattaunawar zaman lafiya tsakanin bangarorin Yemen da aka shirya a kasar Sweden.

Bayan mako guda da shirin tuntubar juna a kasar Sweden, bangarorin da ba sa ga maciji da juna a Yemen sun amince za su dakatar da yakin da suke yi a yankin tashar ruwa ta birnin Hudaydah wanda ke hannun 'yan tawaye, inda miliyoyin 'yan kasar Yemen suka dogara kan abinci da man fetur da ake shigarwa yankin daga ketare.

Sai dai Lowcock ya yi gargadin cewa, akwai wasu matakai masu yawa da suka dace a dauka duk kuwa da irin nasarorin da aka cimma yayin tattaunawar Sweden.

"Tun da farko a yau na jagoranci wani taron tattaunawa game da batun Yemen tare da dukkan manyan jami'an MDD da sauran jami'ai masu lura da hukumomin samar da tallafin jin kai. Bisa ga abin da muka binciko shi ne, labari mai dadi da muka samu a wannan makon har yanzu ba shi da wani tasiri ga miliyoyin al'umma wadanda ke bukatar tallafi," ya fadawa taron majalisar. "Darrusan guda biyu ne: akwai yiwuwar a samu nasarori, amma dole muna bukatar yin aiki tukuru a halin yanzu."

Lowcock, wanda ya ziyarci Yemen kwana baya, ya ce yanayin bukatar agajin gaggawa a kasar ya yi matukar tsananta.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China