in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Trump ya ce kasarsa ba ta gaggawar tattaunawa da Koriya ta Arewa
2018-12-15 15:23:10 cri

Shugaba Donald Trump na Amurka, ya ce kasar sa ba ta cikin gaggawar ci gaba da tattaunawa da kasar koriya ta Arewa. Shugaban wanda ya wallafa hakan a shafin sa na tweeter a jiya, ya ce Koriya ta Arewa na da gangariyar dama ta bunkasa tattalin arzikin ta, kuma shugaban ta Kim Jong Un ya fi kowa fahimtar hakan.

Shugaba Trump ya yi wannan tsokaci ne game da batun tattaunawar Amurka da Koriya ta Arewa a 'yan watannin baya bayan nan. Kasashen biyu dai na da banbance banbance tsakanin su, game da batun aiwatar da manufar raba zirin Koriya da makaman kare dangi, da batun takunkumin Amurka kan Koriyar, da kuma batun yarjejeniyar kawo karshen yake yake.

A baya bayan nan dai an soke tattaunawar da aka tsara yi tsakanin Mr. Pompeo da wani babban jami'in Koriya ta Arewa, ko da yake dai an danganta hakan da matsalar lokaci.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China