in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wasu kalmomi masu muhimmanci game da tattalin arzikin Sin a 2019
2018-12-14 18:57:28 cri

A jiya Alhamis ne ofishin siyasa na kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin ya gudanar da wani taro, a inda aka tattauna ayyuka masu alaka da tattalin arzikin kasar Sin a shekarar 2019. Bisa la'akari da yanayi mai sarkakiya da duniya ke ciki a halin yanzu, makomar tattalin arzikin Sin a shekara mai zuwa zai shafi kasar Sin, gami da karuwar tattalin arzikin duniya. Sai dai bisa bayanan da aka gabatar bayan taron, ana ganin cewa akwai wasu kalmomin da suka dace mu mai da hankali a kansu.

Na farko: neman ci gaba a cikin yanayi na kwanciyar hankali

A shekarar 2019 ne za a cika shekaru 70 da kafa jamhuriyar jama'ar kasar Sin, kana wa'adin da aka sanya game da burin kafa al'umma mai cikakkiyar walwala a kasar Sin na karatowa. Saboda haka, yadda za a tsaya kan kokarin neman ci gaba gami da kasancewa cikin yanayin da ya dace na da ma'ana sosai.

Taron na wannan karo, ya ce ya kamata a kara samar da guraban ayyukan yi, da tabbatar da tafiyar da harkokin tattalin arziki da cinikin waje yadda ya kamata, da kara jawo jarin waje da zuba jari a ketare ta hanyar da ta dace. Taron ya kuma bukaci a raya tattalin arziki lami lafiya da tabbatar da zaman lafiya tsakanin zamantakewar al'umma, al'amuran da suka shaida cewa, shugabannin jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin suna da kyakkyawar fahimta game da halin da ake ciki a gida da waje sosai, da kuma kokarin bullo da dabaru don tinkarar su. Musamman a daidai wannan lokacin da ake kara fuskantar takaddamar siyasa a fadin duniya, kana, ake kara samun abubuwan rashin tabbas game da ci gaban tattalin arziki, raya tattalin arziki ta hanyar da ta dace na da matukar muhimmanci ga kasar Sin.

Kalma mai muhimmanci ta biyu: samun ci gaba mai inganci

A jawabin da ya gabatar a gun bikin baje kolin kayayyakin da ake shigo da su kasar Sin da ya gudana a farkon watan Nuwamban da ya wuce, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bayyana cewa, yanayin da tattalin arziki ke ciki a gida da kuma waje, kasar Sin ita ma ta fuskanci matsaloli, sai dai ya jaddada cewa, matsaloli ne da aka fuskanta a lokacin da tattalin arziki ke bunkasa, kuma muna kokarin daukar matakan daidaita su, matakan da suka fara amfani.

Matakin da shugaba Xi Jinping ya ambata kuma shi ne samun ci gaba mai inganci. Taron ofishin siyasa na kwamitin kolin jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin a wannan karo ya yi nuni da cewa, al'umma za su kara amfana daga ci gaba mai inganci da ake kokarin ganin an tabbatar.

A shekarar badi, Sin za ta ci gaba da yin kwaskwarima kan tsarin samar da kayayyaki bisa bukatu, da tsarin kasuwanni, da kara bude kofa ga kasashen waje, da bullo da tsarin tattalin arziki na zamani, kana za ta yi kokari wajen magance manyan hadurra, da daukar hakikanan matakai na yaki da talauci, da yaki da gurbata yanayi, da raya sha'anin kera kayayyaki, da yin kwaskwarima kan tsarin tattalin arziki, da inganta rayuwar jama'a da sauransu.

Na uku: a tsaya tsayin daka kan manufar da aka tsara.

Shekarar bana shekaru 40 ke nan da kasar Sin ta fara aiwatar da manufar bude kofa ga kasashen waje da yin kwaskwarima a cikin gida. A wannan shekara, Sin ta riga ta gabatar da sabbin matakan bude kofa ga kasashe waje.

Manufar bude kofa ga kasashen waje da yin kwaskwarima kamar juyin juya halin kasar Sin karo na biyu ne, wadda ta kawo babban canji ga kasar Sin, har ma ga dukkan duniya gaba daya.

Kasar Sin tana neman raya kanta bisa halin da take ciki, duk wani kalubalolin da kasashen waje suka kawo mata, ba za su canja shirin da kasar Sin ta tsara wajen neman ci gaba ba.

Ko da yake, Sin tana fuskantar kalubaloli da dama, amma tana tsayawa tsayin daka kan fannoni guda uku wajen neman ci gaban tattalin arzikinta, wadanda suka hada da, tattalin arzikin Sin yana ci gaba cikin yanayin da ya dace, ana kuma neman ci gaban tattalin arziki mai inganci, a karshe, za a ci gaba da raya tattalin arzikin kasar cikin yanayi mai kyau. Baya ga haka, an sake sanar da irin wannan bayani a yayin taron ofishin siyasa na kwamitin tsakiyar JKS na wannan karo.

Gabannin bude wani sabon shafin yin kwaskwarima a gida da kuma bude kofa ga waje a kasar Sin, ya kamata kasashen duniya su yi imani kan bunkasuwar tattalin arzikin kasar Sin a nan gaba. (Bello, Murtala, Lubabatu, Zainab, Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China