in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta yi kira da a kara ba mata da yara abinci mai gina jiki
2018-12-14 11:17:09 cri
Wani kudurin MDD da aka amince da shi a jiya, ya yi kira da a kara inganta ba mata da yara abinci mai gina jiki.

Kudurin mai taken, 'kiwon lafiya da sabon tsarin: samar da lafiya a duniya ta hanyar abinci mai gina jiki" ya bukaci kasashe mambobin majalisar, su aiwatar da tsarin ba iyaye mata da jarirai da kuma kananan yara abinci mai gina jiki.

Ya kuma karfafawa kasashen gwiwar karewa da samar da isasshen abinci ga mata da 'yan mata da kuma yara, musammam yayin da rainon ciki da shayarwa, a lokacin da bukatar sinadaran gina jiki ke karuwa, tare da mayar da hankali musammam ga ranaku 1,000 na farkon samun juna biyu har zuwa shekaru 2.

Har ila yau, kudurin, ya yi kira ga kasashen su inganta tare da taimakawa dorewar aikin gona da inganta huldar kasa da kasa domin saukaka cinikayyar albarkatun gona. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China