in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ana ci gaba da tuntubar juna yayin da tattaunawar Cinikayya ke kara fadada tsakanin Sin da Amurka
2018-12-14 09:23:19 cri
Ma'aikatar kula da harkokin cinikayya ta kasar Sin, ta ce tattaunawar cinikayya takanin Sin da Amurka na kara samun ci gaba, yayin da bangarorin biyu ke tuntubar juna akai-akai.

Yayin wani taron manema labarai a jiya, kakakin ma'aikatar Gao Feng, ya ce kasar Sin na maraba da wakilan Amurka, da su kawo mata ziyara domin tattaunawa, kuma a shirye take ita ma jami'anta su ziyarci Amurka.

Gao Feng ya ce kasashen biyu sun cimma matsaya kan wasu batutuwa, ciki har da amfanin gona da makamashi da ababen hawa. Ya ce la'akari da yadda ake matukar bukatarsa, waken soya ya kasance muhimmamin nau'in amfanin gona da Amurka ke kawowa kasar Sin.

Ya kara da cewa, za a fitar da karin bayani game da tattaunawar nan gaba.

Mataimakin Firaministan kasar Sin Liu He, wanda a yanzu haka ke jagorantar tattaunawar cinikayya tsakanin Sin da Amurka, ya tattauna da jami'an Amurkar a ranar Talata, kuma bangarorin biyu sun yi musayar ra'ayi game da yadda za a aiwatar da matsayar da shugabannin kasashen biyu suka cimma da kuma jadawali da matakan da za a dauka na kara kaimin tattaunawar. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China