in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wang Yi ya gana da wakilin farko a kasar Sin na AU
2018-12-13 20:26:38 cri

Mamba a majalisar gudanarwar kasar Sin, kuma ministan harkokin wajen kasar Wang Yi, ya gana da wakilin kungiyar hadin kan Afirka ta AU na farko a nan kasar Sin Rahmat Allah Mohamed Osman, kuma ya karbi takardar nadin jami'in.

Wang Yi ya yi wa Osman maraba da zuwa kasar Sin, inda ya bayyana cewa, shawarar ziri daya da hanya daya, da muradun raya kasashen Afirka nan da shekarar 2063, suna da manufa iri guda, don haka ya kamata sassan biyu su hada kai ta hanyar aiwatar da shawarar ziri daya da hanya daya. Wang Yi ya yi fatan wakilin mai ofishi a kasar Sin, zai taka rawa wajen bunkasa hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka.

A nasa bangare, Osman ya bayyana cewa, kungiyar AU tana goyon bayan shawarar ziri daya da hanya daya da kasar Sin ta gabatar, saboda shawarar ta dace da moriyar kasashen Afirka.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China