in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ma'aikatar wajen Sin: An kama wasu 'yan kasar Canada su biyu bisa tanajin doka
2018-12-13 18:48:29 cri

Yau Alhamis kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Lu Kang, ya bayyana yayin taron ganawa da manema labarai da aka saba yi a nan birnin Beijing cewa, jami'an tsaron kasar Sin, sun riga sun kama 'yan kasar Canada guda biyu, wadanda ke gudanar da aikin gurgunta tsaron kasar bisa tanajin doka.

Jami'in ya ce ana tuhumar 'yan asalin kasar ta Canada su biyu, wato Michael Kovrig, da Michael Spavor, da gudanar da aikin da ka iya zama barazana ga tsaron jamhuriyar jama'ar kasar Sin, a don haka bisa dokar babban laifin kasar Sin, jami'an hukumar kiyaye tsaron kasa ta birnin Beijing, da hukumar kiyaye tsaron kasa ta birnin Dandong na lardin Liaoning, sun kama wadannan mutane biyu karkashin tanajin doka a ranar 10 ga watan nan.

Ya ci gaba da cewa, hukumar kiyaye tsaron kasa ta Beijing, da hukumar kiyaye tsaron kasa ta lardin Liaoning, sun riga sun gabatar da rahoto mai nasaba da batun, ga ofishin jakadancin kasar Canada dake nan kasar Sin, haka kuma ana kiyaye hakkin su yadda ya kamata.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China