Da suke bayani game da alkawarin da suka dauka a lokacin taron gidauniyar neman taimakon kudaden da aka shirya a birnin Geneva, a daidai lokacin da duniya ke fama da yanayi mai sarkakiya sakamakon tashe tashen hankula, hukumar ta UNHCR ta sanar da cewa, wadannan alkawurra na farko farko muhimman alamu ne dake nuna yiwuwar samun kudaden da ake bukata don gudanar da ayyukan jin kan.
A cewar hukumar UNHCR, halin da duniya ta tsinci kanta a yau na samun sabbin mutane dake kauracewa matsugunansu, da kuma dimbin tashe tashen hankulan da suka ki ci suka ki cinyewa suna cigaba faruwa babu kakkautawa.
Hukumar MDD ta bayyana cewa, a lokaci guda ana fama da karin sabbin matsalolin da suka hada da sauyin yanayi, talauci da rashin daidaito, suna daga cikin dalilan dake kara ruruta wutar rikice rikice, wadanda daga bisani suke kara haifar da karuwar sabbin mutanen dake kauracewa matsugunansu domin neman mafaka a wuraren da aka kebewa 'yan gudun hijira. (Ahmad Fagam)