Wata sanarwar da hukumar ta fitar ta ce kudaden wanda babban sashen bada agajin gaggawa na MDD wato (CERF) ya samar da su, za'a yi amfani da kudaden wajen daukar matakan dakile yiwuwar barkewar annobar Ebola domin hana cutar bazuwa a kasashen dake makwabtaka da jamhuriyar demokaradiyyar Kongo (DRC).
"Hukumomin kai daukin gaggawa, wadanda hukumar lafiya ta duniya (WHO) ke jagoranta, suna yin aiki tukuru wajen ganin an dakile bazuwar annobar cutar ta Ebola a gabashin DRC, amma abu ne mai matukar muhimmanci a tallafawa kasashen dake makwabtaka da Kongon. Samar da kudade a kan lokaci da hukumar CERF ta yi yana da muhimmanci, hakan zai yi matukar tasiri wajen hana kwayoyin cutar yaduwa a makwabtan kasashe," in ji Lowcock. (Ahmad Fagam)