in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi ya gana da bakin da suke halartar dandalin kasa da kasa na Imperial Springs na 2018
2018-12-12 20:48:03 cri

Yau Laraba shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya gana da bakin da suke halartar dandalin kasa da kasa na Imperial Springs na shekarar 2018, wadanda suka zo nan kasar ta Sin daga kasashen waje. Shugaba Xi ya bayana cewa, sakamakon da kasarsa ta samu tun bayan da ta fara aiwatar da manufar gyaran fuska a gida da bude kofa ga ketare, da kuma sabbin muhimman matakan da kasarsa za ta dauka, domin kara bude kofa ga kasashen waje. Haka kuma ya yi cikakken bayani kan huldar dake tsakanin kasar Sin da sauran kasashen duniya, daga baya ya saurari rahotannin da bakin suka gabatar a yayin ganawar ta su.

Xi ya jaddada cewa, kasar Sin ta fi mai da hankali kan moriyar al'ummunta, kuma za ta ci gaba da nacewa ga manufar yin gyaran fuska a gida da bude kofa ga ketare a nan gaba, a don haka ta gabatar da shawarar ziri daya da hanya daya, domin samar da sabuwar damar yin hadin gwiwa tsakanin kasa da kasa, tare kuma da gina kyakkyawar makomar bil Adama.

Kungiyar sada zumunta ga kasashen waje ta kasar Sin, da kungiyar sada zumunta dake tsakanin Sin da Autralia ne suka kafa dandalin kasa da kasa na Imperial Springs cikin hadin gwiwa a shekarar 2014, inda a kan gayyaci shahararrun tsoffin 'yan siyasa, da masana, da 'yan kasuwa domin su halarci dandalin. Babban taken dandalin na bana shi ne "gyaran fuska da bude kofa, da hadin gwiwa da kuma samun moriya tare".(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China