in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin tana daukar hakikanin matakin kare hakkin dan Adam
2018-12-12 19:03:42 cri

Yau Laraba kasar Sin ta fitar da wata takardar gwamnati mai taken "ci gaban da kasar Sin ta samu a fannin kare hakkin dan Adam, tun bayan da ta fara aiwatar da manufar gyaran fuska a gida da bude kofa ga ketare kafin shekaru 40 da suka gabata", inda aka yi cikakken bayani kan sakamakon da kasar ta Sin ta samu a fannin kare hakkin dan Adam a cikin wadannan shekaru 40, haka kuma aka jaddada cewa, domin cimma burin kare hakkin dan Adam na al'ummun kasar, gwamnatin kasar Sin ta yi kokarin sabunta tunanin aikinta bisa bukatar sauyin yanayin da take ciki.

A bayyane take cewa, an lura kasar Sin ta samu wata hanyar kare hakkin dan Adam da ta dace da yanayin da kasar ke ciki, ta kuma samar da sabbin fasahohi da sakamakon kare hakkin dan Adam a tarihin wayewar kan bil Adama.

Kwanan baya shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya aika sakon murnar kira taron tattaunwa domin tunawa da cika shekaru 70 da fitar da "sanarwar hakkin dan Adam ta duniya" a nan birnin Beijing, inda ya yi nuni da cewa, rayuwar al'ummun kasa mai zaman jituwa da wadata, ita ce hakkin dan Adam mafi muhimmanci. Shugaba Xi ya taba gabatar da ra'ayinsa kan aikin kiyaye hakkin dan Adam, ya ce ya kamata a hada ka'idar kare hakkin dan Adam da hakikanin yanayin da ake ciki, ta yadda za a samu wata hanya da ta dace da yanayin da kasar ke ciki, haka kuma za a kara mai da hankali kan moriyar al'ummun kasar yayin da ake gudanar da aikin kare hakkin dan Adam, ra'ayin da ya samu karbuwa matuka daga wajen daukacin al'ummun kasar.

Kamar yadda takardar gwamnatin nan ta bayyana, a cikin shekaru 40 da suka gabata, kasar Sin tana kokarin kare hakkin dan Adam, da tabbatar da hakkin dan Adam, da kuma ingiza aikin kare hakkin dan Adam, yayin da take aiwatar da manufar gyaran fuska a gida da bude kofa ga ketare, haka kuma gwamnatin kasar ta rubuta batutuwa masu nasaba da hakan a cikin tsarin mulkin kasar, da kuma shirin raya kasa. Ana iya cewa, kasar Sin tana gudanar da aikin kare hakkin dan Adam a matsayin ka'ida mai muhimmanci, yayin da take gudanar da harkokin kasa.

Game da wannan batu, shugaban kasar Jamus Frank-Walter Steinmeier da ya kai ziyara a kasar Sin a kwanakin baya, ya bayyana wa shugaba Xi Jinping cewa, bayan da ya kai ziyara a wurare daban daban na kasar Sin, ya gamsu da kuma yabon nasarorin da Sin ta samu a fannonin tattalin arziki da zamantakewar al'umma a cikin shekaru 40 da fara bude kofa ga kasashen waje da yin kwaskwarima, musamman cimma nasarar kawar da talauci na Sinawa fiye da miliyan 100.

A nasa bangare shugaban bankin duniya Kim Yong ya bayyana cewa, a cikin shekarun 40, Sin ta samu nasarori da dama wajen yaki da talauci a tarihin dan Adam, kuma fasahohin Sin za su taimakawa sauran kasashen duniya wajen kara samun ci gaba.

Takardar sha'annin hakkin dan Adam ta Sin ta yi bayani a fannonin rayuwar jama'ar Sin, da hakkin dan Adam na Sinawa, da ikon dukiya, da ikon aiki, da ikon tabbacin zamantakewar al'umma, da ikon samun ilmi, da ikon al'adu, da ikon yin zabe, da ikon bin addini da sauransu, kana ta yi nuni da cewa, Sin ta kyautata ikon kungiyoyin musamman, kamar kananan kabilu, da harkokin mata, da yara, da tsofaffi, da nakasassu da sauransu. Hakan na nuna cewa Sinawa sun fi samun cikakken hakkin dan Adam a halin yanzu.

A cikin shekaru 40 da suka gabata, Sin ta taka wata hanyar raya hakkin dan Adam dake dace da yanayin kasar, yayin da take yin kokarin bude kofa ga kasashen waje da yin kwaskwarima. A shekaru 40 masu zuwa har ma a nan gaba, Sin za ta kara tabbatar da hakki da 'yanci da zaman jin dadin jama'a, yayin da take kara yin kokarin bude kofa ga kasashen waje da yin kwaskwarima, da kuma kara samar da gudummawa wajen raya sha'anin hakkin dan Adam na duniya gaba daya.(Jamila Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China