in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An ba da belin 'yar kasar Sin da kasar Canada ke tsare da ita
2018-12-12 13:59:41 cri
A jiya Talata, alkalin babbar kotun lardin British Columbia na kasar Canada ya sanar da amincewar ba da belin sako Madam Meng Wanzhou, babbar darektar kula da harkokin kudi na kamfanin Huawei na kasar Sin.

Bayan da Canada ta kama Madam Meng Wanzhou a ranar 1 ga wata kamar yadda Amurka ta bukata, Sinawa mazauna kasar ta Canada da ma mutane masu rajin ganin an gudanar da adalci daga sassa daban daban sun bayyana damuwa da rashin jin dadi, inda suka bukaci a sako Madam Meng nan da nan.

Baya ga haka, wasu 'yan kasashen yammaci masu basira da sanin ya kamata sun yi bayanai ta kafofin yada labarai, inda suka yi nuni da cewa, dalilin da ya sa Amurka ta bukaci Canada ta kama Madam Meng Wanzhou shi ne don neman dakile kamfanin Huawei, ta yadda za ta kawo cikas ga ci gaban kasar Sin ta fannin fasahar sadarwa ta 5G. Kuma wannan matakin babu kunya a ciki, haka kuma mataki ne na kariyar ciniki. (Lubabatu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China