in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Aikin kiyaye 'yancin mallakar fasaha na kara taka rawa wajen sanya kasar Sin zama kasa mai kirekire-kirkire
2018-12-12 15:05:46 cri

Jiya Talata, ofishin watsa labaru na majalisar gudanarwar kasar Sin ya shirya taron manema labaru game da ci gaba da sauye-sauyen da kasar ta samu a fannin kiyaye 'yancin mallakar fasaha a cikin shekaru 40 da fara aiwatar da manufar yin gyare-gyare a cikin gida da bude kofa ga kasashen ketare. Rahotanni daga taron na cewa, kasar Sin ta zama kasar dake kan gaba a fannin 'yancin mallakar fasaha, kana aikin kiyaye 'yancin mallakar fasaha na kara taka rawa wajen mayar da kasar a matsayin kasa mai fasahar kirkire-kirkire.

Ci gaban da aka samu a cikin shekaru 40 da fara aiwatar da manufar yin gyare-gyare a cikin gida da bude kofa ga kasashen ketare, ta sa kasar Sin zama wata babbar kasa mai 'yancin mallakar fasaha. Alkaluman kididdiga na nuna cewa, a shekarar 2017, kayayyakin dake neman mallakar fasaha a kasar sun kai miliyan 1 da dubu 382, hakan ya sa kasar Sin ta ci gaba da zama a sahun gaba a duniya a cikin shekaru 7 da suka wuce a jere. Kana kayayyakin da kasar Sin ta gabatar dake neman 'yancin mallakar fasaha ta duniya ta hanyar yarjejeniyar hadin kan tambarin kaya sun kai dubu 51, wato ta haura zuwa matsayi na biyu a duniya. Baya ga haka, jimillar kudin amfani da 'yancin mallakar fasaha da ake fitarwa ta kai dalar Amurka biliyan 4.786, saurin karuwarta yana gaba a fannin cinikayyar ba da hidima a duk kasar.

A yayin taron manema labarun, babbar jami'ar kula da 'yancin mallakar fasaha ta kamfanin Lenovo madam Chen Yuanqing ta bayyana cewa, 'yancin mallakar fasaha na kara taka muhimmiyar rawa wajen inganta karfin kamfanonin kasar Sin wajen yin takara a kasuwannin duniya. A shekarar 2012, kamfanin Lenovo ya kaddamar da wata irin kwanfutar tafi da gidanka ta farko a duniya dake iya jujjuya ta zuwa digiri 360, amma ba da dadewa ba, sai aka gano cewa, akwai masu takara a duniya da suka gaje irin wannan kayan a bikin baje kolin kasa da kasa. To, yaya za a hana masu takara a duniya kwaikwayon kayan kamfanin Lenovo? Madam Chen ta ce,

"Ko da yake an kaddamar da irin wannan kaya ne a shekarar 2012, amma a yayin da ake gwada wannan kayan a shekarar 2005, mun shirya sosai wajen neman 'yancin mallakar fasahar kayan. A karshe dai, mu yi amfani da 'yancin mallakar fasaha da tambarin kayan dake hannunmu, saboda fadi tashi da wadanda ke takara da mu, hakan ya sa ba a kaddamar da wannan kwamfuta a kasuwar duniya ba a tsakanin shekarar 2012 zuwa shekarar 2014. Wannan ya nuna cewa, 'yancin mallakar fasaha ya taimaka wa irin kayan da kamfanin Lenovo ya kera ta yadda ya samu fifiko a duniya har shekaru biyu."

Tun daga shekarar 2011 zuwan yanzu, yawan kayayyakin da kasar Sin ta gabatar na neman 'yancin mallakar fasaha ya kai matsayin farko a duniya a cikin shekaru 7 da suka wuce a jere, a shekarar 2016 kuma, ya wuce jimilar na Amurka, da Japan da Koriya ta kudu da kuma kungiyar EU baki daya. Ban da wannan kuma, ingancin kayayyakin da kasar ke neman 'yancin mallakar fasaha shi ma na kyautatuwa, tsohon shugaban sashen kula da yarjejeniyoyi da dokoki na hukumar kula da 'yancin mallakar fasaha ta kasar Sin mista Yin Xintian ya bayyana a yayin taron manema labarun cewa,

"Ko shakka babu bai kamata mu sa ran alheri kan yawan kayayyakin da muke neman 'yancin mallakar fasaha kawai ba, ya kamata mu yi kokarin inganta ingancin kayayyakin da muka gabatar na neman 'yancin mallakar fasaha, wato mu kara matsayin kimmiya da fasaha na kayayyakin. Wannan ya jawo hankalin hukumar kula da 'yancin mallakar fasaha ta kasar sosai. Yanzu gwamnatin kasarmu ta dauki jerin matakai a wannan fanni, da nufin murkushe wadancan kayayyaki marasa ingancin fasaha. Na yi imanin cewa, idan aka samu tsari mai inganci, za a samu kyautatuwar dangantaka a tsakanin yawan kayayyakin da kuma ingancinsu."

A cikin 'yan shekarun da suka gabata, ta hanyar matakan kara ingancin kayayyaki dake neman 'yancin mallakar fasaha, da kara kokarin samar da kayayyaki masu daraja, kasar Sin ta samu muhimman fasahohi a fannin 'yancin mallakar fasaha a fannonin zirga-zirgar jiragen sama da sararin samaniya, da jiragen kasa masu saurin gaske, da kuma makamashin nukiliya da dai sauransu. A matsayinta na kasa mai kula da 'yancin mallakar fasaha na kamfanoni, babbar jami'ar kamfanin Lenovo madam Chen Yuanqing ta bayyana cewa, tana sa ido da ganin ci gaban da za a samu a fannin 'yancin mallakar fasaha a nan kasar Sin. Ta ce,

"Mun gano jerin matakan da kasar Sin ta dauka na kara ingancin kayayyaki masu neman 'yancin mallakar fasaha, da kara kokarin samar da kayayyaki masu daraja, tare kuma da inganta amfani da fasahohi masu inganci kan ayyukan yin kirkire-kirkire, wadanda za su sanya aikin 'yancin mallakar fasaha kara taka rawa wajen yin kirkire-kirkire." (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China