in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta fitar da rahoto kan nasarar da ta samu na kare hakkokin bil'adama tun bayan fara aiwatar da manufar bude kofa
2018-12-12 11:07:10 cri
Kasar Sin ta fitar da wani rahoto a hukumance a jiya Laraba, wanda ya bayyana irin nasarorin da ta samu a fannin kare hakkokin bil'adama tun bayan fara aiwatar da manufar gyare-gyare a gida da bude kofa ga kasashen waje.

Rahoton mai taken "nasarar da aka samu wajen kare hakkokin bil'adama cikin shekaru 40 da fara aiwatar da manufar gyare gyare da bude kofa ga kasashen waje a kasar Sin" ya ce manufar ta taimaka wajen 'yantarwa da samar da ci gaban ma'aikata a cikin al'umma, sannan ya bude wani sabon babi ga ra'ayin gurguzu mai halayyar musammam ta kasar Sin, da kuma ci gaban hakkokin bil adama.

Ya ce cikin shekaru 40, al'ummar Sinawa sun yi aiki tukuru karkashin shugabanci mai karfi na JKS, kuma an samu manyan sauye-sauye baya ga ingantuwar yanayin zaman rayuwa.

Rahoton ya kara da cewa, a ko da yaushe, JKS kan ba bukatu da muradun jama'a muhimmanci, da tabbatar da mutane sun aiwatar da gyare-gyare da kansu, domin su ci gajiyarsu tare.

Har ila yau, rahoton ya ce kasar Sin ta gudanar da tarin musaya da hadin gwiwa dangane da kare hakkokin bil'adama, kuma ta kiyaye hakkokin bil'adama na kasa da kasa da suka wajaba a kanta. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China